Zaman Sasanci da Y’an Ta’adda a Faskari: Yadda Abin Yake

top-news



Daga Yusuf Suleiman K/Soro

Biyo bayan kace-nace kan maganar sasanci da y’an ta’adda da akace gwamnati tayi a Karamar Hukumar Faskari, akwai bukatar a fahimci wasu abubuwa masu muhimmanci don aje kowace kwarya a gurbin ta. Shin wace gwamnatin ce ta dauki matakin duba da cewa akwai Gwamnatin Tarayya kuma akwai ta Jiha? Hakan zai haska ma al’umma yadda dambarwar take ganin yadda wasu suka fahimci abin a baibai tare da kallon kamar Gwamnatin Jihar Katsina na tubka da warwara a dalilin  cewa Gwamna Malam Dikko Umar Radda yasha shan alwashin cewa bazai zauna sasanci da y’an ta’adda ba. Kai karewa ma, har shan alwashi yayi cewa koda kudin Jihar Katsina kan shawo matsalar tsaro, ba zaiyi kasa a guiwa ba wajen ganin ya karar da su don sama ma jihar zaman lafiya da walwala. 

Na shigo cikin wannan dambarwar ne ganin cewa da ni akayi yawon neman samun nasarar Maigirma Gwamna Radda, kuma ina da masaniya bakin gwargwado na alkawurran da ya dauka na kare mutunci da martaba al’umma, cikin su, har da na rashin barin harkar tsaro ta zama harka da y’an ta’adda ke damawa asha yadda suka ga dama. Ganin yadda ake ta kace-nace kan zaman da akace anyi a Fankama ta Karamar Hukumar Faskari, har ana k’ok’arin nuna cewa Gwamna Radda yayi kasa a guiwa wajen cika alkawarin rashin sasanci da y’an ta’adda yasa naga ya dace in tsoma baki saboda fahimtar ba haka abin yake ba.

A k’ok’arin gano yadda maganar take, na baza koma wajen neman sahihan bayanai na yadda abinda yake, kuma na samu natsuwa da cewa alkawarin Gwamna Radda na nan; ko gezau. Hasali ma, wannan zama da akace anyi, zama ne da babu hannun gwamnatin Jihar Katsina a ciki don dama faduwa ce tazo daidai da zama. Na farko dai dama harkar tsaro ba hurumin gwamnoni da jihohin su bane. Na biyu kuma, dama  Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Radda bata da ra’ayin bata lokaci da kudi wajen sulhu da y’an ta’adda tunda a baya anyi ba daya, ba biyu ba kuma duka babu inda kwalliya ta biya kudin sabulu. Fahimtar haka ya kara man wajibcin yin wannan rubutu don kauda zargin gazawa da naga wasu na yi akan gwamnatin Jihar Katsina a hannu daya, a dayan hannun kuma in goge zargin cin amana da naga wasu nayi ma Gwamna Radda ba tare da cika sharuddan bincike da yanke hukunci ba. 

Da farko dai akwai bukatar mu fahimci cewa harkar tsaro, harka ce da gaba daya a karkashin hurumin Gwamnatin Tarayya kundin tsarin mulkin Najeriya ya aje harkar. Gwamnatin Tarayya ita keda wuka da nama a maganar tsaro. Ita ke iko da jami’an tsaro kuma ita ke da hurumin tsarin yadda za’a tafiyar da harkar tsaro a fadin kasa baki daya. Kundin tsarin mulki bai ba Gwamna ikon sayen koda bakan da ko na, ballantana bindiga, da sunan tsaro ba. Yadai ba gwamnoni damar bama Jami’an tsaro tallafi na kudi suyi abinda suka ga ya dace don inganta tsaro. Duk da cewa Gwamna a Jiha shi ke da ikon yanke hukunci kan lamurran Jiha, wannan ikon bai hada da maganar tsaro ba. Duk wani abu da gwamnan Jiha zai yi kan maganar tsaro tallafi ne na sa kai don ya taimaka ma jami’an tsaro su cike gibin da ka iya samuwa wajen tafiyar da aikin su har aga an shawo kan matsalo. 

Kenan, ba abin mamaki bane idan Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda, yace bazai zauna sasanci da y’an ta’adda ba amma Gwamnatin Tarayya ta ga ribar zama da su har ta zauna da su din. Mai yiwuwa Gwamna Radda ya kalli abin daga mahangar gara ya ba jami’an tsaro gudummuwa maimakon ya zauna sasanci da y’an ta’adda ya basu kudi — wanda ansha yin hakan a baya amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba. 

Abin nufi, maganar sasanci da ake cewa anyi a Karamar Hukumar Faskari da y’an ta’adda, bayanai masu sahihancin wadanda har a faifan bidiyo akwai, sun tabbatar abu ne da Gwamnatin Tarayya ta assasa don kashin kanta, kuma ba tare da hannun Gwamnatin Jihar Katsina ba. Wannan kuma ba laifi bane duba da cewa a wuyanta nauyin samar da tsaro ya rataya kamar yadda bai zama laifa idan Maigirma Gwamna, Malam Dikko Radda, yace bazai zauna sasanci da y’an ta’adda ba. Da gwamnatin Jiha da ta Tarayya duk suna da hurumin daukar matakin da suka dauka. A takaice, babu inda sasancin Gwamnatin Tarayya da y’an ta’adda yaci karo da matsayar Gwamna Radda ta rashin yarda da zaman sasanci da su. Wannan shine abinda Bahaushe ke ce ma bikin Magaji bai hana na Magajiya. 

Duk dai zaman lafiya ake nema kuma duka bangarorin biyu na da damar bin hanyar da suka ga tafi dacewa a samu zaman lafiyar. Matsayar da kowannen su kuma zai dauka tana daidai da yadda ya dace da matsugunnin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya aje shi. Wannan kuma ba yana nufin babu hadin kai tsakanin gwamnatocin biyu bane. A’a! Dama ce da marubutun kundin tsarin mulki suka ba shugabanni a matakai mabanbanta na daukar matakai mabanbanta don zaton ko za’a dace.

NNPC Advert