NA ZIYARCI IN DA AKA FARA RUWAN DUFANA, DA YA HALAKAR DA MUTANEN ANNABI NUHU(AS)
- Katsina City News
- 19 Sep, 2023
- 2144
@ Katsina times
@ jaridar taskar labarai
Kufa wani gari ne, dake kilomita dari da 170 daga Baghdad Babban birnin kasar Iraq.
A gefen garin kufa, akwai inda nan ne,aka fara ruwan Dufana wanda ya halakar da mutanen Annabi Nuhu(as).
kamar yadda yazo acikin alkur ani mai tsarki a suratul Nuhu.
Alkur ani ya bada labarin ruwan ya fara daga kasa ne, sai kuma sama ta barke da ruwa.
Mutanen Annabi Nuhu (as)Allah ya tseratar dasu ta wani jirgin ruwa da Allah ya umurci Annabi Nuhu (as) ya sassaka.
Ruwan Rijiyar tun zamanin Annabi Nuhu take bubbuga sama da shekaru dubu uku har yanzu.
An gyara wajen, maziyarta na zuwa daga koina a duniya.
Naje wannan rijiya,nasha ruwanta, na kuma nayi guzurinsu zuwa Najeriya.