Ranar Kin Shan Taba Ta Duniya: Ma'aikatar Lafiya ta jihar Katsina ta fadakar kan illolin shan taba sigari

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17062025_203619_FB_IMG_1750192508078.jpg

Auwal Isah Musa | Katsina TIMES 



Ma'aikatar lafiya ta jihar Katsina, ta fadakar game da illoli, lahanin da cututtukan da shan taba sigari ke haifarwa ga lafiyar al'umma.

Kwamishinan lafiya na jihar, Alhaji Musa Adamu ne ya yi wannan fadakarwar, a cikin wani jawabi da ya gabatar a yayin taron manema labarai kan tunawa da "Ranar Kin Shan Taba Sigari Ta Duniya" wanda ma'aikatar ta kira a ma'aikatar a ranar Talatar nan, taron da Jaridun KatsinaTimes da sauran jaridu suka shaida.

A jawabin da ya gabatar a wajen, Kwamishin lafiyar ya bayyana cewar, a matsayinsu na wadanda alhakin kula da lafiyar al'ummar jihar ya rataya a wuyansu, dole ne su fadakar da al'ummar irin illolin da shan taba sigari ke haifarwa ga lafiyar al'ummar wadanda har ma suke kai wa ga salwantar da rayukansu.

A saboda haka, Kwamishinan ya yi kira ga al'ummar jihar da masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wajen wayar da kan al'umma illar shan taba sigari, inda ya ce wannan na a matsayin "aikin gayya da hada hannu da karfe domin mu zabi lafiyar al'ummarmu."

Ya ce; "Babban abin da muke muhimmantarwa a irin wannan rana shi ne wayar da kan al'umma game da da hadarin da ke tattare da shan taba sigari, wadda take mummunar illa ga lafiyar al'umma".

Adamu, ya ce kowa ya san irin cututtuka masu wuyar magani da al'umma ke fama da su kamar cutar Daji, Cutar Zuciya, Bugun Jini, Cututtukan Hunhu da sauransu, inda ya bayyana cewar akasarinsu suna da alaka da shan Taba Sigari.

"Kowace shekara fiye da mutane Miliyan 8 ke mutuwa sakamakon cututtun da ke da alaka da Taba sigari." Ya koka

Musa Adamu, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu masana'antu da kamfanunuwa ke amfani da hanyoyi daban wajen jan ra'ayin musamman matasa zuwa ga shan Taba Sigari, wanda ya bayyana hakan a matsayin illa babba ga goben matasanmu.

"Al'ummar jihar Katsina yau rana ce ta aikin gayya da hada hannu da karfe domin mu zabi lafiyar al'umma, ba biyan bukatar kamfanoni ba kan sha'anin Taba." In ji shi

Ya kara da cewar, domin "Idan aka samu ingantattun lafiyayyun matasa, to al'umma tana da rayuwa mai inganci a gaba." Ya nusar.

Daga karshe, kwamishinan ya jadda kokarin da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ke yi, wajen ganin ta inganta harkar lafiya a katafanin al'ummar jihar.

Taron manema labaran ya samu halartar mambobin kungiyar inganta mu'amala da jama'a da Majalisun Dokoki, wadanda suke hadin gwiwa da ma'aikatar lafiyar wajen wayar da kan al'umma kan illar shan Taba Sigari.

An dai ware ranar 31 ga watan Mayu na kowace shekara a matsayin "Ranar Ƙin Shan Taba Sigari ta Duniya", domin wayar da kan al'umma game da illolin shan taba sigari, bayyana dabarun da masana'antun tabar ke amfani da su, da kuma aika kiranye-kiranyen yadda za a kauracewa shan taba sigarin, wanda takenta na bana shi ne: "Taba na kisa, Mu guje ta".

Follow Us