Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES
Gwamnatin Jihar Katsina ta jinjinawa Kungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) kan rawar da ta taka wajen ci gaban kasa da kare dimokuraɗiyya, yayin bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafa ta a dakin taro na Hayatt Regency Suite a garin Katsina, ranar Talata 17 ga watan Yuni 2025
A jawabinsa, da ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda, Ph.D., Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Dr. Bala Salisu Zango, ya jaddada irin tasirin da 'yan jarida ke da shi a tarihin Najeriya – tun daga fafutukar neman 'yancin kai zuwa tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya.
“Cikar NUJ shekaru 70 ba wai biki ne kawai ba, lokaci ne na tunani da duba baya,” in ji Dr. Zango. “Ya kamata mu kalli inda muka fito, inda muke yanzu, da kuma inda muke nufi.”
Ya bayyana damuwarsa kan yadda kafofin sada zumunta ke lalata martabar aikin jarida, inda ya ce fiye da kashi 60 cikin 100 na masu kiran kansu 'yan jarida ba su da horon sana'a. “Aikin jarida sana’a ce ba kawai 'yanci ba. Yana bukatar horo, ɗabi’a da kwarewa,” in ji shi.
Dr. Zango ya kara da cewa Gwamnatin Katsina na ci gaba da tallafawa 'yan jarida ta hanyar shirye-shiryen horo da ɗaukar nauyin shirye-shiryen kafofin watsa labarai a cikin jihar. Ya bukaci 'yan jarida da su rika bayar da rahotannin gaskiya da wadanda za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da hadin kai, musamman a bangaren tsaro wanda gwamnatin jihar ke bai wa muhimmanci.
Dr. Balarabe daga Kwalejin Kimiyya ta Hassan Usman Katsina ya gabatar da muhimmin takarda mai taken: “NUJ a Shekaru 70: Duba Tarihi.” A cikin takardarsa, ya raba tarihin kungiyar NUJ zuwa matakai biyar:
1. Zamanin Kafa (1955–1960) – Lokacin da NUJ ta fara aiki da kishin kasa da adawa da mulkin mallaka.
2. Bayan Samun ‘Yancin Kai (1960s–1970s) – Jarida ta zama hanya ta wayar da kan al’umma da tallafa wa cigaban kasa.
3. Lokacin Matsin Lamba (1970s–1999) – Lokacin mulkin soja, NUJ ta fuskanci hare-hare, tsare 'yan jarida da dokoki masu tsauri.
4. Lokacin Dimokuraɗiyya (1999–Yanzu) – Jarida ta taka rawa wajen sa ido kan gwamnati da kare muradun jama’a.
5. Zamanin Intanet – Kalubale ya karu saboda yaduwar labaran karya da rashin tsari a kafafen sada zumunta.
Shugaban NUJ na Jihar Katsina, Mannir Dan Ali, ya bayyana cewa tun daga kafuwar NUJ a 1955 har zuwa 2025, shekaru 70 kenan na kishin kasa, aiki tuƙuru da hidima ga Najeriya. Ya gode wa tsofaffin shugabannin kungiyar da suka assasa tubalin ci gaba.
Ya ce taken wannan biki shi ne “NUJ a Shekaru 70: Duba Tarihi,” kuma an gayyato malami kuma tsohon ɗan jarida, Dr. Sama'ila Balarabe daga Kwalejin Kimiyya ta Katsina, domin gabatar da takarda.
Babban jigo kuma mai masaukin baki, UK Bello Kankara (Hakimin Ketare), wanda shi ne Uba na kungiyar NUJ a Katsina, ya jinjinawa shugabannin NUJ musamman na Katsina bisa gyaran ofishin NUJ da masallacin kungiyar.
Ya kuma bayyana farin cikinsa kan karramawar da zai samu daga NUJ Abuja a ranar Asabar, 21 ga watan Yuni. Kankara ya bayyana tarihin aikinsa tun daga shekarar 1975, lokacin da ya fara aiki a gidan rediyon Kaduna, kafin daga bisani ya shiga hukumar kwastam a matsayin jami’in hulɗa da jama’a (PRO).
“Ina alfahari da kasancewa cikin wannan gida har yanzu,” in ji shi. “Ina fatan NUJ za ta ci gaba da bunƙasa cikin nasara da ɗaukaka.”
Bikin ya kasance lokaci na nuna godiya, nazari kan tarihi da kuma kiran da'a ga 'yan jarida da hukumomi, domin tabbatar da ingantaccen aikin jarida na kishin kasa da gaskiya.