Manoma Sun Zargi Kwamitin Gandun Daji na Katsina da Kwace Gonaki, ...Tare Da Nuna Fargaba Kan Barazanar Tsaro

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13062025_143857_FB_IMG_1749825399201.jpg



Daga Auwal Isah Musa, Zaharaddee Ishaq Abubakar 

Kungiyar manoma daga yankin Barawa/Shibdawa da ke karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina sun koka da matukar damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin korar gaggawa da rashin adalci daga gonakin da suke nomawa, wanda suka ce kwamitin kula da gandun daji da shata iyaka na jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Halilu Bako ne ya aikata musu hakan.

A yayin taron manema labarai da suka kira ranar Litinin, wanda wakilan jaridar Katsina Times da wasu kafofin watsa labarai suka halarta, manoman sun bayyana cewa duk da cika sharuddan noma a filayen, ciki har da samun sahalewar gwamnati da kuma biyan haraji na naira dubu 15 a duk shekara, kwatsam sai aka umarce su da su fice daga wuraren. Sun ce an shaida musu cewa Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ne ya bayar da umarnin.

“Mun riga mun gyara gonaki, mun sa taki, wasu ma sun fara shuka. Sai aka ce mu tashi mu bar wurin. Wannan abu bai dace ba, kuma yana da wata makarkashiya,” in ji wani daga cikin manoman.

Manoman sun bayyana fargabarsu kan yadda wannan matakin ka iya dawo da matsalar tsaro a yankin. Sun ce a da lokacin da yankin ke daji, ‘yan bindiga na cin karensu babu babbaka, suna sace mutane da kashe-kashe. Amma tun da suka fara noma a wuraren, an samu kwanciyar hankali.

Sun kara da cewa suna da sahihan bayanai cewa wasu sabbin mutane za a kawo su ajiye a wuraren, wadanda suke zargin suna da alaka da ‘yan bindiga. “Muna da tabbacin cewa wasu daga cikin mutanen da za a kawo sansani a wuraren suna da alaka da miyagun ‘yan bindiga. A matsayimmu na mazauna yankin, ba mu yarda da hakan ba,” in ji su.

A cikin wani kiran neman taimako, manoman sun roki Gwamna Radda da ya shiga cikin lamarin da gaggawa, domin a cewarsu, wannan mataki bai dace da tsare-tsaren gwamnatinsa ba na bunkasa noma da yaki da rashin tsaro. “Ba mu yadda cewa wannan umarni daga gwamna ne ba. Gwamnatin sa ta jajirce wajen inganta noma da tsaro. Muna ganin akwai wadanda ke kokarin zagon kasa ne kawai,” in ji daya daga cikin shugabannin kungiyar.

“Muna rokon Gwamna Dikko Radda da ya dauki matakin bincike a kan wannan lamari. Mu kuma ba ma son abin da zai sa mu ji kunya daga gwamnati da muke marawa baya,” suka jaddada.

Taron ya samu halartar wakilan manoma daga kauyuka da dama kamar Barawa, Shibdawa, Tantagarya, Sabon Gari, Walawa, ‘Yar Tsamiya, Shekar Gabi da sauransu. Haka zalika, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki sun halarta ciki har da: Sakataren kungiyar DSP Aliyu Mamman, Shugaban kungiyar Manoma da masu kiwon kaji na jihar Katsina Alhaji Abbati Dahiru, Kwamandan Vigilante na yankin Muntari Kudi-Kasa, Dakta Salisu Abdullahi, Danjuma Shibdawa, Shugaban gamayyar kungiyoyin matasa Awwal Shu’aibu, Tijjani Ibrahim Bakiyawa, da Limamin Masallacin Rafin Dadi, Musa Yusuf Dahiru.

Sai dai da muka tuntubi shugaban kwamitin, Alhaji Halilu Bako, ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa duk wani fili da gwamnati ke bada damar noma, sai dai ‘yan asalin yankin ne ke cin moriyarsa, tare da bin dukkan ka’idoji na gwamnati.

Follow Us