SHEKARU DARI DA TIS'IN (190) DA WAFATIN SARKIN KATSINA MUJADDADI MALAM UMARUN DALLAJE

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27052025_111349_FB_IMG_1748343942093.jpg

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN


Rai baƙon Duniya, dukkan abin da Allah ya bayar nasa ne, haka kuma dukkan abin da ya karɓa shima nasa ne.

A yau Shekaru Ɗari da Chasa'in dai-dai da Wafatin Mujaddadi Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje (190)

Malam Umarun Dallaje, fitaccen Malamin addinin Musulunci, kuma ɗaya daga cikin jagororin yan gwagwarmaya masu jihadin jaddada addinin Musulunci a ƙasar Hausa.

A Rana mai Kamar ta yau 25 ga watan Mayu na  Shekara ta 1835 Miladiyya, Allah ya karɓi Rayuwar Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje ( Mujaddadi ) A Katsina.

Malam Umarun Dallaje Ya rasu yanada shekaru Sittin da Biyar (65) a duniya, a cikin waɗannan Shekarun nasa masu albarka, ya yi ƙoƙari matuƙa gaya, wajen Hidimtawa addinin musulunci, domin neman yardar Allah.

An haifi Malam Umarun Dallaje a shekarar 1770, a cikin wata rugar Fulani dake Dasije, cikin ƙaramar Hukumar Bindawa ta jihar Katsina.

 ASALI DA NASABA:

Zuriyar da Malam Ummarun Dallaje ya fito daga cikin ta, asalin su Larabawa ne masu magana da harshen larabci daga inda suka fito.

Yau da gobe, waɗannan mutane saboda cuɗanya da juna da zama wuri ɗaya yasa sun zama masu harshe iri ɗaya.

Kakannin Malam Ummarun Dallaje, zama ya kai su wuraren daban-daban, inda suka samar da jinsin ƙabilar Fulani Ba'awa (Fulani Ba'awiyya) sune tushen wannan ƙabila.

Wannan Zuriya Allah ya albarkar kace ta da Mutane masu yawa da arzuƙin dabbobi, sannan kuma ga ilimin addini da jarumta, shiyasa duk wajen da suka safka ake maraba da zuwan su.

Su kuwa Fulani, asalin su sun fito daga zuriyar Nasi ɗan Uƙba ne, Shi kuwa Uƙba, tarihi ya nuna shine mafarin jinsin ƙabilar Fulani duka, kuma shima asalin sa balarabe ne.

Dangane da salasala kuwa, kowa yasan yanda balarabe mutum yake da ƙoƙari wajen kiyaye nasabar Kakannin sa duk inda ya ke a duniya.

1. Abdul-wahab
2. Muhammadu Na'i
3. Abubakar
4. Abdulmuminu
5. Ummarun Dallaje

Wannan shine abin da muka iya samu daga cikin wani littafin tarihi na (Machika Abdu Dogo)

 Kishin gida da asali da addini Sunna ce ta Manzo S.A.W

 HIJIRA:

Kakannin Malam Ummarun Dallaje, sunyi hijrah daga inda suke ta dalilai na yaƙe-yaƙe da rashin jituwa tsakanin Sarki Abdulkarimu ɗan Yamen jikan Yaƙub, wanda ya hamɓarar da mulkin Sarki Dawud na ƙabilar Tunjurawa a cikin shekara ta 1681-1707.

Kakan Malam Umarun Dallaje mai suna Muhammadu Na'i yana daga cikin jarumai da suka Gwabza wannan yaƙi da shi ne aka fara kuma da shine aka ƙare, a wancan lokacin yana daga cikin mutanen da ake alfahari da su a wannan nahiya.

Daga ƙarshe Sarki Abdulkarimu ya yi nasara, sai Muhammadu Na'i ya yi Hijira daga wannan gari nasu na Wadai zuwa Daular Borno.

ZUWAN SU DAULAR BORNO:

A lokacin da suka isa, sun tarar da Mai Dunama vii ne ke mulkin Daular Borno wajejen 1711.

Samun labarin zuwan Muhammadu Na'i a Daular Borno da jama'ar sa, ya sanya mutane da dama sun gaza samun nutsuwa da shi, saboda labarin sa ya kai ko'ina na irin jarumtar yaƙi da yake da ita a wannan zamanin.

Bayan wani lokaci sai MAI DUNAMA ya yi shawara da mutanensa, inda ya sallami muhammadu Na'i cikin mutuntawa tare da girmamawa, ya kuma haɗa masa Sha Tara ta arziƙi, su kayi ban kwana suka ƙara matsawa zuwa gaba.

A cikin wannan yanayin ne suna cikin tafiya rai ya yi halin sa, Muhammadu Na'i ajali ya yi kira, daman kuma shekarunsa sun yi nisa da yawa.

Daga Wannan lokacin ne ɗan sa Abubakar ya cigaba da jagorantar ayarin, har Allah yasa suka iso GURU a nan suka yi masauki kafin su wuce zuwa gaba.

ZUWAN SU KASAR KATSINA:

Zuriyar Dallazawa sun iso ƙasar Katsin a cikin ƙarni na 17, zamanin Sarkin Katsina Usman Tsaga Rana 1673. 

Tarihi ya cigaba da nuna cewa, wasu daga cikin ayarin, sun haƙura sun zauna wajen da Muhammadu Na'i ya rasu, domin su cigaba da rayuwa.

Wasu kuma sun matso zuwa gaba, har Cikin ƙasar Gwambe Aba, wasu kuma sun koma Borno inda wasu daga ciki suka ida isa ƙasar Katsina.

Garin da basu ji daɗin zaman sa ba, shine wani gari da wasu ƙabilu na Ɓata ko Ɓachama suka rinƙa neman janyo fitina, inda daga ƙarshe dai suka gusa zuwa gaba, domin neman zaman lafiya da kauce wa zubar da jini.

Waɗannan mutane sun zauna wurare da dama, inda kuma suka yaɗa zuriya da yawa a bisa hanyarsu ta tafiya, kuma duk garin da suka je suna ajiye mutum ɗaya domin ya cigaba da karantarwa ga jama'ar garin kafin su wuce zuwa gaba.

Yawancin su malamai ne masana masu ba da karatu, haka kuma suma suna cigaba da ƙara neman ilimin a duk inda suka ji labarin wani fitaccen malami a duk inda yake.

Wannan ne dalilin yasa malam Ummarun Dallaje bayan ya samu labarin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya tafi domin ƙara neman ilimin addini, saboda haka shi Ummarun Dallaje daman can tun kafin Shehu ya yi kira ga ayi jihadi almajirin sa ne. Shiyasa suka shaƙu da Muhammadu Bello Sosai ɗan Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Malam Ummarun Dallaje yana daga cikin almajiran Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da aka yi gwagwarmaya domin  kira tare da jaddada addinin musulunci a yankunan ƙasar Hausa baki ɗaya.

Akwai yaƙe-yaƙen da aka yi da shi, irin yaƙin Tafkin kwatto a  shekarar 1804, da shi ne Kuma aka yi na Alwasa inda aka samu gagarumar nasara a waɗannan yankuna.

Waɗannan nasarori da aka samu, daga nan ne Muhammadu Bello ɗan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, ya umurci malam Ummarun Dallaje, da sauran mabiyansa da su ɗaura ɗamarar jihadi domin jaddada addinin musulunci a ƙasar Katsina.

ZAMAN MALAM UMARUN DALLAJE A MATSAYIN SARKIN KATSINA 1807:

Bayan an ƙare jihadi, Sarakunan Katsina na Haɓe sun gudu zuwa Dankama har ƙasar Maraɗi. Sai shi kuma Malam Umarun Dallaje ya shiga gidan sarautar katsina ya kafa daular Fulani. 

Malam Ummarun Dallaje, bayan ya shiga gidan sarautar katsina ya tarar da wasu kayan sarauta, da Sarakunan Haɓe ke amfani da su, ya kuma adana su ya basu muhimmanci domin tunawa da tarihi. 

 Kayan Tarihin su ne:

* Wuƙa Bebe
* Wuƙa Gajere
* Tukunyar ƙarfe
* Gwabron Tambari

Ta sanadiyyar wannan ne, Katsinawa su ke da kayan tarihi da ake alfahari da su, kuma ake amfani da su wajen naɗa sabon Sarkin Katsina a yau. Malam Ummarun Dallaje bai lalata ɗaya daga ciki ba ko rusa wani gini da ya tarar an yi, kamar masallacin Gobarau da shi kansa gidan sarautar katsina ɗin.

Malam Ummarun Dallaje, ya yi mulki irin na tarayya. Inda ya naɗa kowane daga cikin magoya bayansa lokacin jihadi, domin su taimaka masa wajen gudanar da sha'anin mulki da taimakon al'umma.

Malam Ummarun Dallaje, shine sarkin da ya yi fice wajen ƙarfafa sha'anin addinin musulunci, wanda ya samu rauni lokacin sarakunan da suka shuɗe na Haɓe.

Malam Ummarun Dallaje, mutum ne karimi mai karamci tare da karrama mutane, ya yi ƙoƙari sosai wajen haɗa kan mutanen ƙasar sa ta Katsina, ya kuma tilasta bin ƙa'idojin addinin musulunci sau da ƙafa a ƙasarsa, a inda ya sa aka rinƙa bi lungu da saƙo domin tabbatar da cewa mutane suna gudanar da ibada yanda yakamata musamman yin salloli guda biyar a kowace rana, wanda kuma duk yake gwaro ya isa aure aka tilasta masa yin aure.

Malam Ummarun Dallaje, ya gina masallatai da makarantun karatun Alƙur'ani a birane da ƙauyuka, domin waɗannan sune aiyukan da shuwagabanni ko sarakuna da suke mulki yakamata su yi, musamman ma, wajen ƙarfafa shari'ar Musulunci da kare ƙasa daga mahara domin jin daɗin al'umma tare da walwalarsu.

Waɗannan abubuwa da Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje ya yi ya sa ƙasar Katsina ta ƙara kafuwa bisa diga-diganta a inda talakawa da masu sarautar da ke ƙasar Katsina, suka riƙa ɗaukar kansu a matsayin Katsinawa masu Sarkin Katsina a Birnin Katsina, batare da nuna banbanci ba.
 
A zamanin Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje, martabar malamai ta bunƙasa sosai a cikin Birnin Katsina da ƙauyuka.

A dalilin haka, malamai suka ci-gaba da kwararowa a Birnin Katsina, addinin musulunci ya ƙara kafuwa a waɗannan yankuna, inda malaman suka zama tamkar su ne Sarakunan da ke faɗa a ji, saboda irin yanda Ummarun Dallaje yake girmamawa agare su.

Haka kuma, manyan yan kasuwa da ƙanana, su ma sun yi Allah son barka ga Sarkin. Baƙi kuma aka rinƙa basu ƙasar noma da wajen da za su zauna da iyalansu, da hakane Katsina ta cika ta tumbatsa.

Mafi yawan Katsinawa ba ƙi ne, daga wani wuri suka zo, ko dai ta dalilin neman ilimin addini ko fatauci. Shiyasa daga wannan lokacin ne aka rinƙa yi ma garin Katsina kirari *( Katsina Ɗakin* *Kara )*  saboda mutane ne masu karimci tare da karrama jama'a.

MALAMAI MASU JIHADIN JADDADA ADDININ MUSULUNCI A ƘASAR HAUSA:

1. Malam Ummarun Dallaje (Katsina)
2. Malam Sambo Ɗan Ashafa (Zamfara)
3. Malam Isyaku (Daura)
4. Malam Musa (Zazzau)
5. Malam Sulaimanu (Kano)
6. Malam Ibrahim Ɗantunku (Kazaure)
7. Malam Ibrahim Zaki (Katagum)
8. Malam Goni Mukhtar (Misau)
9. Malam Muhammadu Wabi (jama'are)
10. Malam Buba Yero (Gwambe)
11. Malam Yakubu (Bauchi)
12. Malam Adama (Adamawa)
13. Malam Dendo (Bida)
14. Malam Muhamman (Haɗejia)

Dukkan waɗannan malamai sun yi amfani da Alƙur'ani da Hadisi ne wajen yin Jihadin su, babu ɗaya daga cikinsu wanda jihadinsa ya saɓa ma koyarwar Alƙur'ani ko Sunna.

Zuriyar Dallazawa sun yi mulki na adadin shekaru Ɗari dai-dai suna bada irin tasu gudammawa musamman akan abin da ya shafi addini.

SARAKUNAN DALLAZAWA:

1. Malam Ummarun Dallaje (1807-1835)

2. Sarkin Katsina Malam Abubakar Saddiƙu (1835-1844)

3. Sarkin Katsina Malam Muhammadu Bello (1844-1869)

4. Sarkin Katsina Malam Ahmadu Rufa'i Garnaƙaƙi (1869-1870)

5. Sarkin Katsina Malam Ibrahim (1870-1882)

6. Sarkin Katsina Malam Musa (1882-1887)

7. Sarkin Katsina Malam Abubakar (1887-1905)

8. Sarkin Katsina Malam Yero (1905-1906)

Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje ya rasu ya bar matan aure da ya'ya Ashirin da Ɗaya a Duniya.

Malam Ummarun Dallaje, mutum ne mai son zumunci da kuma aikata shi a aikace, ta hakane ya aurar da ya'yan sa mata ga wasu gidajen aminnan sa sarakuna kuma malamai masu jihadi, domin ƙara ƙarfafa zumunci a tsakanin gidajen.

Daga cikin ya'yan nasa Mata sune kamar haka.

1. Magajiya Zulaihatu

 Ta auri Malam Buba Yero Mujaddadi kuma Sarkin Gwambe wanda Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya ba Tutar jaddada addinin musulunci a yankin ƙasar Gombe.

 Ita ta haifi sarkin Gombe Suleimanu, wanda ya yi sarauta a shekara ta 1842-1844.

2. Magajiya Aminatu Aya

Ta auri Sarkin Maska Sani 1864-1881

Ita ta haifi Sarakunan Maska Uku kamar haka.

Sarkin Maska Ummaru 1881-1888

Sarkin Maska Halilu 1888-1910

Sarkin Maska Shehu Autan Aya 1915-1928

3. Magajiya Maryamu Hanatari

 Ta auri Galadima Abdullahi 1821-1861

Ita ta haifi Galadima Shawai wanda ya yi sarautar Malumfashi a shekara ta 1861-1894

4. Magajiya Nana Asma'u

Ta auri Ƙaura Abubakar 1811-1854

Ita ta haifi Ƙaura Halilu wanda ya yi Sarautar Rimi a shekara ta 1889-1895

Kabarin Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje yana nan Bayan gidan Sarkin Katsina, tare da na wasu daga cikin ya'yan sa sarakunan da suka gaje shi, a ɓangare ɗaya kuma akwai kabarin amininsa Galadima Dudi a wurin.

Allah ta'ala ya jikansa ya ƙara jaddada Rahma agare shi tare da sauran dukkan musulmi baki ɗaya.

 Allah shine mafi sani a kan dukkan komai.

Zaharaddin Ibrahim
Mayanan Safana

#masarautarkankiya 
#katsinawa 
#arewa

Follow Us