Tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Kwamitin Gudanarwa na TETFUND, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya kasance cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka halarci babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Taron ya samu halartar fitattun shugabannin jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, wanda ya sake jaddada kudurin gwamnatin tarayya na sauya fasalin bangaren gidaje da raya birane a fadin kasar nan.
Rt. Hon. Masari, wanda aka sani da kwarewa a fagen shugabanci, ya gabatar da muhimman bayanai da suka danganci muhimmancin zaman lafiya, adalci da gina jam’iyya mai ingantaccen tsari. Ya jaddada cewa dole ne a samar da jam’iyya mai cike da gaskiya da rikon amana domin tafiya daidai da tsarin dimokuraɗiyya.
Taron ya kasance dandalin tattaunawa da musayar ra’ayi kan makomar jam’iyyar APC a matakin jihohi da ƙasa baki ɗaya. An mayar da hankali kan yadda za a ƙarfafa haɗin kai, karfafa matasa da kuma fuskantar manyan kalubale na siyasa da shugabanci.
Masari da sauran manyan baki sun bayyana cewa haɗin gwiwa da gogaggun shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen cimma nasarori masu ɗorewa da bunƙasa ƙasa.
Al’ummar Jihar Katsina da ma Nijeriya gaba ɗaya na fatan cewa irin waɗannan tarurruka na manyan jiga-jigan jam’iyya za su taka rawa wajen kai ƙasar nan zuwa tudun mun tsira.
Hoto: Shamsu Yunusa Dogoru