Rabon Motoci: Gwamnan Zamfara Ya Yaba Wa Hon. Adamu Mai Palace.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21052025_105733_IMG-20250521-WA0067.jpg



Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jinjina wa ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Gusau/Tsafe, Hon. Kabiru Amadu ‘Mai Palace,’ bisa samar da romon Dimokraɗiyya ga al'ummar Mazabar sa.

A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da wani ƙasaitaccen biki a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau, inda aka raba wasu motoci guda 100, waɗanda suka haɗa da motocin hawa da kuma taraktocin noma.

Kamar yadda ya ke a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau jiya Lahadi, ya bayyana cewa an raba waɗannan motoci ne ga shugabannin jam'iyya, Dattawa, masu faɗa a ji da kuma wasu zababbu daga Mazabar tasa.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, ko a makon da ya gabata Hon. Kabiru Amadu ya raba mababura 100 ga wasu zababbun mutane.

Saboda wannan ƙoƙari na Hon. Kabiru, Gwamna Lawal ya jinjina masa matuƙa, tare da yin kira ga sauran 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki kan su mayar da hankali wajen kyautata rayuwa da jin daɗin jama'a.

Gwamna Lawal ya ce, “Ina matuƙar nuna farin ciki na da jin daɗi bisa wannan habbasa ta Hon. Kabiru Amadu wajen gudanar da abubuwan da za su amfani jama'ar Mazabar sa. Wannan abin a yaba ne, tatre da ƙarfafa masa gwiwa.

“A yayin da gwamnatin jiha ta duƙufa wajen aiwatar da inganta harkokin gyaran makarantu, asibitoci da hanyoyi, duk da haka akwai buƙatar samar da shirin da zai habbaka ƙoƙarin mu. Wannan kuma shi ne abin da Hon. Mai Palace ke yi.

“A shekaru biyu da muka yi a kan mulki, mun samu gagarumar nasara a fannonin ilimi, tsaro, kiwon lafiya, jin daɗin ma'aikata da gyara birane, da dai sauran su da dama.

“Za mu ci gaba da haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki don samun nasarar shirin gwamnatin mu na ceto Zamfara. Ina godiya ga Hon. Kabiru Amadu bisa taimakon da ya ke mana, tare da ba shi tabbacin samun goyon bayan mu.

Tun farko a nasa jawabin, Hon. Kabiru Amadu ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya ke aiwatar wa al'ummar sa. sun haɗa da bayar da tallafin kuɗaɗen karatu da samar da guraben ƙaro ilimi.

“Ina kashe Miliyoyin Naira ga al'ummar mazaba ta a fannin biyan kuɗin makaranta da kuma samar da guraben karatu ga ɗaliban mu.

“A watan da ya gabata, na bayar da sama da babura 100 ga wasu zababbun mutane, musamman matasa, don a sauƙaƙa masu zirga-zirgar su ta yau da kullum. Ƙari ga waɗannan motoci da na ke rabawa a yau, na kuma samar da taraktoci da sauran kayan noma ga manoman mazabar Gusau/Tsafe, a ƙoƙarin mu na habbaka harkar joma."

Follow Us