Sabbin Tsare-tsaren Masarautu Hudu a Katsina: Malamin Jami’a Ya Gabatar da Tsari Bisa Tsarin Tarihi da Yankuna

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20052025_090803_FB_IMG_1747732028232.jpg



Daga Dr. Waisu Iliyasu, Sashen Tarihi da Nazarin Tsaro, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina

Wani masani a fannin tarihi daga Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina, ya fitar da wata sabuwar hanya wacce za a iya amfani da ita wajen tsara sabbin masarautu hudu a Jihar Katsina. Wannan tsari ya kunshi rarraba kananan hukumomi da gundumomi zuwa sabbin masarautu da za su kasance bisa la’akari da tarihi, al’adu da zamantakewar yankuna.

Manufar wannan tsari ita ce taimakawa masu tsara manufofi da ‘yan majalisar dokoki da ke da alhakin duba irin wannan batu, musamman ganin yadda wasu al’ummomi suka gabatar da bukatar kafa sabbin masarautu a jihar.

Tsarin ya fito da yadda za a iya raba tsohuwar masarautar Katsina zuwa sabbin masarautu guda hudu tare da bayyana hedikwatocin kowace da kananan hukumomi da gundumomin da za su shiga ƙarƙashinsu kamar haka:

Masarautar Katsina

Hedkwata: Birnin Katsina
Kananan Hukumomi: Katsina, Rimi, Charanci, Mashi, Mani, Dutsi

Gundumomi: Magajingari, Kaura, Majidadi, Sarkin Shanu, Kuraye, Iya, Durbi, Marusa

Masarautar Kankia

Hedkwata: Garin Kankia
Karamar Hukuma: Kankia
Gunduma, Kankia

Sharhi:
Wannan masarauta na da tushe a tarihin mulkin zuriyar Malam Umarun Dalalje, wanda jikokinsa suka riƙe sarautar Kankia da Musawa. Tun zamanin jihadi, yankunan Bindawa, Doro da Kusada sun kasance karkashin ikon danginsa.

Masarautar Dutsin-ma

Hedkwata: Dutsin-ma
Kananan Hukumomi: Dutsin-ma, Safana, Kurfi, Kankara

Gundumomi: Dan Yusufa, Batagarawa, Dan Barhim, Dambo, Ubandoma, Fagaci, Sarkin Musawa, Jikamshi, Bebeji

Masarautar Jibia

Hedkwata: Jibia
Kananan Hukumomi: Jibia, Batsari, Kaita

Gundumomi: Yandaka, Yarima, Gatari, Magajin Malam, Sarkin Fulani Dangi, Maradi, Sarkin Pauwa, Kanwa

Sharhi:
An gabatar da shawarar cewa masarautar za ta dace da zuriyar Malam Umarun Dumyawa, wanda a baya yankunan Jibia da Kaita suka kasance ƙarƙashinsa. Batsari da Batagarawa na da alaƙar tarihi da wadannan yankuna, don haka su ma na iya kasancewa a cikin wannan sabuwar masarauta.

Masarautar Funtua

Hedkwata: Funtua
Kananan Hukumomi: Funtua, Faskari, Bakori, Kafur, Danja, Malumfashi, Dandume, Sabuwa

Gundumomi: Sarkin Maska, Sarkin Yamma, Maiurawa, Makama, Tsiga, Dan Galadima, Danja, Galadima, Daneji, Dandume, Sabuwa

Sharhi:
Masarautar Funtua na iya kasancewa a hannun zuriyar Malam Gudindi daga Malumfashi ko Malam Dudi daga Maska. Duk da cewa ba su da tutar jihadi, tarihin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban yankin ya sanya cancantar su a matsayin shugabanni na masarauta.

Wannan tsari da malamin jami’ar ya gabatar wani mataki ne na nuna yadda za a iya gudanar da sauye-sauye a tsarin masarautun jihar bisa la’akari da tarihi da zamantakewar al’umma, ba tare da la'akari da wani shirin gwamnati ko hukuma ba.

© Katsina Times

Follow Us