KO JAM IYYAR PDP ZATA ZAMA TARIHI NE?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05052025_181351_PDP-12.jpg


Muazu Hassan @ Katsina times 

Wani labari da yake shigo mana mai tushe kuma da zafin sa, shine, wasu daga cikin gwamnonin jam iyyar PDP sun gana da Wike ministan Abuja a satin da ya  gabata.
Majiya Mai tushe ta tabbatar mana cewa gwamnonin sun kaskantar da kansu da walakantar da mutuncin su, suna rokon Wike  ya dawo ayi tafiyar PDP dashi akan kowane sharadi yake dashi.
Majiyarmu tace, Wike ya muzanta bakin nasa, sannan ya kafa masu wasu sharadudda irin wadanda yake bukata.cikin izgili da dagawa.
Majiyarmu tace wasu gwamnonin sun amince da sharruddan na wike wasu kuma sun ce zasu je suyi nazari.
Majiyarmu tace, idan gwamnonin suka amince  da abin da wike ke bukata, to lallai jam iyyar PDP zata shiga kundin tarihi, kamar yadda wasu jam iyyun suka shiga.
Daga sharadin da ake zargi, gwamnonin sun amince dashi, shine, a zaben 2027, PDP ba zata tsayar da Nagartaccen dan takara ba.
Amma a sauran zabubbukan zasu iya tsayarwa su kuma dage in sunci zaben shikenan.
Wike zai tabbatar da duk gwamnan PDP da ya yarda da wannan kaidar in yana neman tazarce zai wuce, in kuma magaji zai nada za a mara masa baya yayi nasara.
Wani labarin kuma da zafin sa, wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da jaridun Katsina times cewa, akwai yiyuwar "yan majalisun tarayya biyu na jam iyyar PDP daga katsina, zasu chanza sheka zuwa APC.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa Magana tayi nisa,kuma ana tsammanin an kammala komai sai shelantawa.
Idan wadannan "yan majalisun biyu suka koma zai zama saura dan majalisa daya watau na mashi da dutsi wanda yake amsa sunan wai yana karkashin jam iyyar PDP ne.

Follow Us