Ƴar Asalin Jihar Katsina Ta Zama Daraktar Kasuwanci a Kamfanin NNPCL

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30042025_073412_IMG-20250430-WA0009.jpg


A wani muhimmin cigaba da ke nuna rawar da Jihar Katsina ke takawa a ci gaban ƙasa, Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), ƙarƙashin jagorancin Bayo Ojulari, ya nada Hajiya Maryam Idris Bagiwa – ƴar asalin Jihar Katsina – a matsayin Daraktar Kasuwanci na Kamfanin.

Hajiya Maryam Idris Bagiwa za ta jagoranci harkokin kasuwancin sayar da ɗanyen man fetur na Najeriya, tare da kula da dabarun ciniki a cikin gida da waje. Wannan mukami da aka ɗora mata yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin ƙasa, kuma yana nuna yadda Jihar Katsina ke ci gaba da samar da shugabanni nagari a matakin ƙasa.

Nadinta ya kasance wata gagarumar nasara gare ta, kuma abin alfahari ne ga al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya. Ana sa ran ƙwarewarta da hangen nesanta za su kawo sabbin dabaru da daidaito a sashen kasuwancin kamfanin.

Allah Ya taya ta riko, Ya ba ta nasara a wannan babban aiki – Ameen.

Follow Us