Danmajalissar Tarayya Mai Wakiltar Katsina Ta Tsakiya Ya Raba Kayan Tallafi Na Miliyoyi Ga Al'ummarsa.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28042025_203017_FB_IMG_1745871764489.jpg



Danmajalissar Tarayya Mai Wakiltar Katsina Ta Tsakiya, Honorabul Sani Aliyu Danlami (Mai Raba Alheri) ya raba wa al'ummarsar Mazabarsa kayan tallafi don bunkasa sana'o'insu.

Taron bada tallafin wanda ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko Katsina a ranar Litinin din nan, ya samu halartar dimbin al'ummar karamar hukumar Katsina, Kansiloli da kwamishinoni, 'yanmalissar dokokin jihar, tsaffin 'yanmalissu har ma da gwamnan jihar, da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC.

Da yake jawabi kan makasudin bayar da tallafin, Honorabul Sani Aliyu Danlami, ya kwatanta lamarin a matsayin koyi daga gwamnan jihar.

"Ina so in kara tabbatar wa gwamnan jihar katsina cewa irin abubuwa na alheri da yake yi don ganin an tallafa wa al'umma, a shirye muke mu ma a wakilci da muke yi na majalissar dokoki; za mu yi bakin iya kokarinmu mu rika tallafawa don ganin mun kara kamawa muna ragewa mai girma gwamnan jihar katsina wasu ayyukan, domin kowa ya san yadda yake fadi-tashi wajen ganin al'umma sun dogara da kawukansu." In ji Danlami.

Danlami, ya kuma yaba wa gwamna Radda kan yadda yake kokari musamman a harkar tsaro, Ilimi da kuma lafiya a fadin jihar.

Da yake jawabi a matsayin babban bako mai kaddamarwa, gwamna Dikko Radda, ya yaba wa Danmajalissar bisa ga wannan namijin kokari, ya kuma yi masa fatan dorewa da irin wannan aiki ga al'ummar karamar hukumar ta katsina, inda ya shawarci sauran takwarorinsa da cewar su kwaikwayi irin wannnan tagomashi daga danmajalissar su ma su aiwatar ga al'ummominsu.

"Irin wannan wakilcin ake so; Idan kun dangwalo kuma ku dangwalawa mutane." Gwamna Radda ya fadi cikin raha.

Kayan tallafin da danmajalissar ya raba a matsayin tallafi sun hada da: Motoci (manya) 20, Motoci Hijet 20, Babura 150, Kekunan diki 150, Injinan Faci 50, Injinan ban-ruwan noman rani 150, da kuma tsabar Kudi na Naira Miliyan 60.

Wadanda aka tallafamawa sun hada da: Shugabanni jam'iyya 351, Shugabannin karamar hukuma 27, Ciyamomi na WARD 12, Mata Exco 32, Sauran Exco 249, Ciyamomi na rumfuna, ciyamomin ciyamomi, masu zabe (delegates), jam'iyyar APC ta karamar hukuma da sauransu.

Wadanda suka shaidi taron bayar da tallafin sun hada da Kakakin majalissar dokokin na jihar, Nasir Yahayya Daura da mataimakinsa, Mukaddashin shugaban jam'iyyar APC na jiha, Alhaji Bala Abu Musawa, danmajalissar dokokin jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar katsina, Alhaji Abu Ali Albaba, shugaban karamar hukumar katsina Honorabil Isah Miqdad wanda ya samu wakilcin mataimakinsa.

Sauran sun hada da: tsohon shugaban karamar hukumar Katsina Alhaji Aminu Ashiru, tsohon Sanatan Katsina, honorabul Hamisu Gambo, 'Yanmajalissu, Kwamishinoni, Kansiloli da sauransu.

Follow Us