Kwamitin tantance 'yan fansho da giratuti na jihar Katsina karkashin shugabancin Dr. Faruk Aminu, ya bayyana cewar tuni gwamnatin jihar ta kammala biyan dukkan basussukan giratuti na wadanda suka aje aiki tsakanin shekaru 4 zuwa 5 na kafin hawan gwamnatin Malam Dikko Umar Radda, sannan kuma yanzu haka kwamitin ya kammala aikin tantance wadanda za a biya na tsakanin watan Agustan shekarar 2023 zuwa Disamban 2024.
Sakataren Kwamitin, Mukhtar Ammani Aliyu ne ya bayyana wa jaridun KatsinaTimes haka a ranar Juma'ar nan, jim kadan da kammala aikin tantancewar.
Ya ce a lokacin da gwamnatin Malam Dikko Radda ta zo, ta tarar da dimbin basussuka na Garatuti na kusan shekaru 4 zuwa 5 da ba a biya ba, inda gwamnan ya kafa kwamiti domin tantance wadannan basussuka don a biya mutane hakkokinsu.
"An kafa wannan kwamiti cikin watan Agusta na shekarar 2023 kuma tun daga nan zuwa yanzu kusan watanni 20 ke nan kan wannan aiki muke yi inda muka kammala a yau" In ji shi.
Ya ce, "A sadda muka zo, mun tarar da ana bin bashin Giratuti tsakanin na jiha da kananan hukumomi ya kai kusan Naira Biliyan 30, wanda mai girma gwamna ya sa mu mu tantance.
"A cikin tantancewar muka ga bashin ya koma Biliyan 23; a ciki akwai wadanda suka mutum a lokacin wadanda bashinsu ya kai kusan Bliyan 5 a jiha da kananan hukumomi, wadanda ke a raye kuma bashinsu ya kai kusan Biliyan 18." In ji Ammani.
Ya ci gaba da cewar, "haka kuma gwamnan ya ce mu kara zama a tantance; kowa ya zo sai an gan shi sannan a biya shi. Yanzu maganar da nake da kai wannan bashi na Biliyan 23 gwamnatin jihar katsina ta biya shi duka!" Ya tabbatar
A cewar Muktar Ammani Aliyu, ya zuwa yanzu kuma kwamitin nasu yana cigaba da aikin tantance wadanda suka aje aiki tsakanin Agustan 2023 zuwa Disamban 2024, inda ya ce zasu hannantawa gwamnati aikin nasu wanda suna fatan ba zai dauki lokaci ba za a biya su hakkokin nasu su ma.