Daura Ta Gamsu da Shirin Tallafa wa Mata, Tana Bada Goyon Baya Cikakke — Sarki Umar Faruk

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24042025_052953_FB_IMG_1745472513552.jpg


Daga: Muhammad Ali Hafizy, @Katsina Times

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Dr. Umar Faruk Umar, ya bayyana cikakken goyon bayan Masarautar Daura ga sabon shirin tallafa wa mata masu karamin karfi Nigeria For Women Project, yana mai cewa: “Zamu tabbatar da cewa mun baku hadin kai dari bisa dari domin amfanar da al'umma.”

Wannan furuci ya biyo bayan ziyarar da tawagar ma'aikatan shirin karkashin jagorancin Hajiya Rabi Muhammad suka kai wa Masarautar Daura da kuma shugaban karamar hukumar Daura a ranar Laraba, 23 ga Afrilu, 2025.

Shirin Nigeria For Women Project wanda ya samo asali daga haɗin gwiwar Babban Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya, tare da tallafin jihohi, na da nufin inganta rayuwar mata da ke da ƙaramin karfi, musamman masu kananan sana’o’i. Hajiya Rabi ta bayyana cewa manufar shirin ita ce bunkasa tattalin arzikin al’umma ta hanyar karfafa mata da dama da ke cikin bukata.

A cewarta, an riga an fara aiwatar da shirin a wasu sassan ƙasar nan, kuma yanzu an zabi ƙananan hukumomi uku a jihar Katsina domin fara shirin. Wadannan sun hada da karamar hukumar Katsina, Daura da kuma Funtua — bisa la’akari da yawan mata da kuma tasirin kasuwanci da ke cikin su.

Hajiya Rabi ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara aiwatar da shirin a hukumomin da aka zaɓa, tare da fatan samun nasarorin da ake bukata.

Shugaban karamar hukumar Daura, Hon. Bala Musa, ya bayyana farin cikinsa da aka zabi karamar hukumar domin aiwatar da shirin, yana mai jinjina ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, bisa namijin kokarin da suka yi wajen samar da shirin. Ya kuma sha alwashin cewa hukumarsa za ta bayar da cikakken hadin kai domin tabbatar da nasarar shirin, ganin irin matsin tattalin arziki da ake ciki a halin yanzu.

Masarautar Daura ta nuna cikakken goyon baya ga shirin, tana mai tabbatar da cewa za ta mara masa baya dari bisa dari domin tabbatar da nasarar sa a fadin karamar hukumar.

Follow Us