Sarautar Yandakan Katsina Tsohuwar Sarautace a Masarautar Katsina domin ta samo asalintane tun lokacin Sarakunan Habe, kuma tun wancan lokacin Yandaka Yana daya daga cikin manyan Hakimmai da suka hada da Gazobi, Yandaka, Durbi da sauransu.
Ma'anar Kalmar Yandaka: Abinda ake nufi da Yandaka shine Yandaka Gidan Sarki, watau amintaccen Sarki wanda keda ikon shiga Turakar Sarki, shine maa nar Yandaka tun lokacin Habe.
A Lokacin Sarakunan Habe, Garin Yandaka Ruma shine hedikwatar Yandaka ta Mulki, kuma Gidan shi na cikin Birnin shine Gidan Yandaka Dake Unguwar Yantaba na Yanzu.
SARAUTAR YANDAKA A LOKACIN JIHADI.
Sarautar Yandakan Katsina Hakimin Dutsinma ta samo asaline tun lokacin Jihadin Shehu Usman Danfodio na karni na Shatara( K19). A lokacin da Malam Na Alhaji da Ummarun Dunyawa da Malam Ummarun Dallaje sukaje Sokoto domin anso Tutar Kaddamar da Jihadi a Kasar Katsina. A lokacin da suka je Sokoto sun amso Tutar wajen Mujaddadi Shehu Usman Danfodio, sai ya umarce su da su biya suyi bankwana da dansa Muhammadu Bello. A Gidan Muhammadu Bello sun dade basu sadu da shi ba, Sai Malam Na Alhaji da Malam Ummarun Dunyawa sukayi gajen hakuri suka cewa Malam Ummarun Dallaje wanda shine karami acikin su ya zauna ya jira Muhammadu Bello, idan ya fito sai ya yi masu bankwana. Daga nan sai su suka tafi, basu dade da tafiya sai Allah ya yi wa Muhammadu Bello fitowa, da ya fito ya tarar da Malam Ummarun Dallaje Yana jiransa, sai yace, Allahu Akbar Malam Ummarun Dallaje Kai Allah yayi wa Sarkin Katsina.
Bayan sun dawo Katsina sai dukkanin su kowa yaja bamgarenshi inda ya gudanar da Jihadi. Shi Malam Muhammad Na Alhaji daya taso sai ya bullowa Katsina ta Yamma, ya shigo da Yaki ta Kofar Yandaka, ya ci Kasashen Ruma, da Zakka da sauransu. Shi kuma Malam Ummarun Dunyawa a bangaren Zandam, da Bugaje, da KAITA da sauransu, anan yafi bada karfi a wajen Jihadin shi, a inda ya mamaye wadannan Kasashen da makwabtansu.
Shi kuma Ummarun Dallaje shi yaci Kasashen Dake tsakiyar Katsina da suka hada da Dallaje, Banye, Rugar Bade da sauransu.
Bayan an kare Jihadi acikin shekarar 1807, sai aka raba mukamai ga shuwagabanin Jihadi, shi Ummarun Dallaje shi ya zama Sarkin Katsina, shi kuma Ummarun Dunyawa ya zama Sarkin SULLUBAWA.
Shi kuwa Malam Muhammad Na Alhaji ana kare Jihadi ya rasu acikin shekarar 1807, sai aka dauko babban dan shi Mai suna Muhammad Dikko aka bashi Sarautar Magajin Malam, ya fara zama Tsauri da Zakka.
Acikin shekarar 1928, ne lokacin da aka nada Yandaka Muhammad Sada II, a matsayin Yandakan Katsina, sai Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya taso daga Katsina yazo Dutsinma kewayen Kasa, sai ya umarci Yandaka Muhammad Sada II, da ya maido da Hedikwatar shi a Garin Dutsinma, saboda itace ke tsakiyar Kasar Yandakan Katsina. Anan zaa fahimci cewa Yandaka Muhammad Sada II shine Yandaka na farko da ya fara zama a Garin Dutsinma. Har ya zuwa yanzu Dutsinma Hedikwatar Yandaka take. Kuma Yandakan Katsina Yana daya daga cikin Hakimmai guda hudu na Masarautar Katsina masu zaben Sabon Sarkin Katsina, sauran sune Kauran Katsina, Hakimin Rimi, Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi, sai Durbin Katsina Hakimin Mani.
TSARIN SUNAYEN WADANDA SUKA YI YANDAKAN KATSINA.
1. Malam Na Alhaji ( founder).
2. Muhammadu Dikko ( Magajin Malam)
3. Namoda (shine aka fara kira Yandakan Katsina)
4. Abubakar Dan Muhammadu Dikko
5. Hassan Dan Muhammadu Dikko
6. Muhammadu Sada I Dan Muhammadu Dikko
7. Sule Dan Muhammadu Dikko
8. Zunairu Dan Abubakar
9. Usman Mani Dan Hassan.
10. Muhammadu Sada II Dan Usman Mani
11. Shehu Dan Usman Mani
12. Muhammadu Lawal Dan Dan Sannabi ( Jikan Yandaka Usman Mani)
13. Abubakar Dan Muhammadu Sada II
14. Balan Goggo Muhammad Dan Muhammad Sada II.
15. Sada Muhammad Sada.
Magaddan Kasar Yandakan Katsina.
1. Yariman Dutsinma
2. Yariman Kuki
3. Gazobin Karofi
4. Magaji Katanga
5. Magaji Tayi
6. Magaji Bagagadi
7. Magaji Dagelawal
8. Magaji Kutawa
9. Magaji Wangarawa
10. Magaji Mahuta
11. Magaji Shema
12. Magaji Nasarawa
13. Magaji Makera
14. Magaji Sanawa
15. Magaji Yanshantuna
16. Karare Dabawa.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.