Ba bukatar 'yan jihar Katsina ne a gaban Yakubu Lado Danmarke ba,- Mustapha Inuwa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18042025_095207_FB_IMG_1744969841998.jpg


Daga Auwal Isah | Katsina Times 

Shugaban yakin neman zaben  dankarar gwamnan jihar katsina a karkashin jam'iyya PDP a shekarar 2023, Dr. Mustapha Inuwa ya bayyana uban gidansa da ya yi wa yakin neman zaben a lokacin, Yakubu Lado Danmarke a matsayin wanda ba al'ummar jihar ce a gabansa ba, inda ya ce son kansa da kasuwancinsa ne kawai ya sa a gaba.

Dr. Mustapha Inuwa ya fadi haka ne a cikin wata zantawa da jaridar KatsinaTimes ta yi da shi, bidiyon zantawar da ya bayyana a shafukan jaridar a ranar Alhamis din nan.

Dr. Mustapha ya ce "na yi da-na-sanin yi wa Yakubu Lado shugaban yakin neman Zabe."

A cewar Mustapha Inuwa, domin ba al'ummar jihar Katsina ba ne a gabansa Yakubu Ladon ba, kawai kasuwancinsa ya sa gaba ba bukatar al'ummar jihar na ya zo ya cece su ba.

"Irin abubuwan da ke faruwa (a tafiyar Yakubu Lado) sai mutum ya yi nadamar a ce yana da hannu cikin abin da ya faru (na dafa masa in ya gano)" In ji shi

"(Ya ta6a fada min cewar) abin da yake tunani ma, irinmu da muke da experience, mu zo yana gwamna in yi masa mataimaki. Na yi dariya, don ban taba jin maganar da ta raina min wayau ba irin wannan." In ji Mustapha

"Sai ya ce ai da ma matsalar dai ai na sani tsakanin gwamna da mataimaki ai magana ce ta kudi; Ni in rike 'federal allocation', Kai na bar maka na 'local government'. Wallahi Tallahi abin da ya ce ke nan" In ji Dr. Mustapha.

A saboda da haka, Mustapha ya bayyana nadamarsa karara kan dafa masa da ya yi a tafiyar tasa, ya kuma yi da-na-sanin haka, muma daga lokacin ya zare hannunsa daga lamurransa.

"Maganar gaskiya nadamar da nake yi, da na shiga a cikin hidimarsa a matsayin dantakarar gwamnan, kuma na san cewar wallahi bai cancanta ba." Ya nanata.

Follow Us