RASHIN TSARO: Safana Tana Cikin Mawuyacin Hali
- Katsina City News
- 17 Sep, 2023
- 1250
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Damuna ta Ja, Amfani yazo, Mutanen Ƙaramar Hukumar Safana sun shiga cikin mawuyacin hali na 'yan Bindiga duba da a daidai wannan lokaci ne amfanin gona yake zuwa gida daga gonaki, 'Yan tadda kuma suna cin karensu babu Babbaka ga manoma masu kwaso amfanin gona zuwa gida.
Katsina Times ta Tattauna da wasu Mazauna garin Unguwar Wake, da Unguwar Salihawa. Dukkanin su, bayaninsu Iri ɗaya ne, yanda ake masu ɗauki Daiɗai a gonaki wasu a kashe wasu a biya kuɗi sana a amsosu. Ko da yake a Unguwar Salihawa Kamar yanda rahotanni suke zo mana, cewa Mutanen Unguwar ko ƙauyen Salihawa sunyi sasanci da 'yan ta'addan, wanda sasancin ya dan samar masu sauki tunda har sukanje gona su debi amfanin gona su kaimasu rabi su rike rabi. "An kama wasu Mutum uku inda suka tafi dasu daga gonar da suke Ɗibar amfanin gona, bayan sun tafi daya daga cikinsu yace shi Dan Kauyen Salihawa ne, sai suka sake shi." Inji wani da muka zanta da shi.
Wani da yake cikin wadanda sukai sasancin ya bayyana mana yanda Sasancin yake shine "Suna masu Noma Kuma suje su debe masu amfanin gona da wasu ayyuka na yau da kullum, sana kuma idan sunyi noma su dunga kaimasu abinda suka debe na amfanin."
Mazauna Unguwar wake su kuwa kamar yanda majiyarmu ta sheda mana, sukam kullum tsinta daidai ake masu, basu zuwa Gona, ballantana su debo amfanin gona, a karshe ma zaman garin ya gagaresu sun dawo cikin garin Safana, majiyar tace hakan ma basu tsira ba, a cikin garin ma na Safana barayin suna shigowa, saboda suna jin sunyi karfi.
Haka labarin yake a wasu yankuna na Kananan Hukumomin Kurfi, Dutsinma, Faskari, Danmusa, Batsari, da Jibiya.
Gwamnan jihar Katsina ya fifita bangaren tsaro fiye da ko wane Bangare na Gwamnatin sa inda ko a kwanannan Gwamnan ya ware wasu maƙuden kudade domin tunkarar tsaron gadan-gadan, shin ko wannan yunkuri na gwamnatin jihar Katsina zaiyi tasiri duba da tsohuwar gwamnatin Aminu Masari ta shekara fiye da shida tana yakar 'Yan taddan da makami, da kuma bude kofar sasanci, amma abin bai yi wani tasiri na azo agani ba, kamar yanda wani mai sharhi ya bayyana?
wwwkatsinatimes.com
08032652765, 014548140