Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty International, ta bayyana matukar damuwa da Allah-wadai kan kisan mutane akalla 51 da 'yan bindiga suka yi a daren jiya a kauyen Zikke, karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato.
'Yan bindigar ba wai kawai sun kashe ba ne, har ma sun kona kauyuka da dama tare da wawure dukiyoyin jama'a a hanyarsu. A cewar Amnesty, cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara da tsofaffi da ba su iya tserewa.
Amnesty ta bayyana wannan hari a matsayin abin kyama da sakaci daga bangaren tsaro, musamman ganin cewa makonni biyu da suka gabata ma an kashe mutane 52 a yankin. Ta bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kan yadda irin wannan hari ke ci gaba da faruwa ba tare da dakile shi ba.
Kungiyar ta ce fadar gwamnati na fitar da sanarwar Allah-wadai kawai ba tare da ɗaukar wani kwakkwaran matski na kare rayukan al'umma ba.
Ko da yake Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin daukar sabbin matakan tsaro don dakile matsalar rashin tsaro, Amnesty ta ce harin na baya-bayan nan ya nuna cewa wadannan matakai ba sa yin tasiri.
Daga watan Disamba 2023 zuwa Fabrairu 2024, Amnesty ta ce an kashe mutane 1,336 a jihar Filato, ciki har da mata 533, yara 263, da maza 540. Baya ga haka, mutane 29,554 ne suka rasa matsuguninsu, ciki har da yara 13,093 da mata 16,461.
Amnesty ta kammala da cewa irin wadannan hare-hare na nuna yadda gwamnati ta bar al’ummomin karkara cikin hadari da rashin kariya, kuma rashin daukar matakin gaggawa yana haifar da asarar karin rayuka da dukiyoyi.