Gwamnatin Katsina Ta Gyara Motocin Gidajen Gyaran Hali A kan Naira Miliyan 5

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11042025_153832_IMG-20250411-WA0025.jpg

Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe zunzurutun kudi har Naira Miliyan Biyar wajen gyaran motocin aiki guda takwas na hukumar gyaran hali ta jihar.

A ranar Laraba da ta gabata ne Kwanturola Umar Baba, shugaban hukumar gyaran hali ta jihar Katsina, ya mika motocin da aka gyara ga wakilan sa daga gidajen gyaran hali daban-daban a fadin jihar.

Gyaran motocin ya biyo bayan roko da hukumar ta yi ga Gwamna Dikko Umar Radda PhD, CON, domin sauƙaƙa gudanar da ayyukansu. Kwanturola Umar Baba ya bayyana cewa an gudanar da gyaran ne ta hanyar amfani da kwararrun kanikawa na hukumar da kuma daliban da ke karatu a cibiyar koyon sana’o’i da ke cikin gidajen gyaran hali na jihar. Wannan mataki ya kara musu kwarin gwiwa da kwarewa.

A cewar ASC Najib Idris Kunduru, Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar gyaran hali ta jihar Katsina, Kwanturola Baba yayin da yake mika motocin, ya yaba da yadda Gwamna Radda ya amsa rokon cikin gaggawa, tare da nuna godiya a madadin shugaban hukumar gyaran hali ta kasa, CGC Sylvester N. Nwakuche, MFR, min. Ya kuma tabbatar da cewa motocin za su kasance cikin kulawa da amfani mai nagarta don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Follow Us