Sojojin Operation Fansan Yanma Sun Kashe Shugaban Ƴan Bindiga "Malam" da Wasu Hudu a Faskari

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11042025_122522_Screenshot_20250411-132126.jpg

Sojojin Operation Fansan Yanma Sun Kashe Shugaban Ƴan Bindiga "Malam" da Wasu Hudu a Faskari

Dakarun rundunar sojin Najeriya masu gudanar da Operation Fansan Yanma sun samu nasarar hallaka wani fitaccen shugaban ƴan bindiga da aka fi sani da suna Malam, tare da wasu mutum huɗu da ake zargin suna cikin tawagarsa a wani samame da suka kai a kan hanyar Kandamba-Faskari, cikin Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne bayan makonni na sintiri da artabu tsakanin dakarun sojin da ƴan bindigar, lamarin da ya kai ga tarwatsa maboyar su. Bayan harin, wasu daga cikin ƴan bindigar sun yi gaggawar binne gawarwakin abokan aikinsu a cikin ramuka masu zurfi, yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka na harbin bindiga.

Bayan cigaba da bincike, sojoji sun gano inda aka binne gawarwakin, ciki har da na Malam da ake zargi da jagorantar ayyukan ta’addanci a ƙananan hukumomin Sabuwa, Dandume, Faskari da Funtua. Majiyoyi daga jami’an tsaro sun bayyana cewa Malam yana da hannu a manyan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, satar shanu, da kai hari kan al’umma da dama a yankin.

Hare-haren da rundunar soji ke kaiwa ya ci gaba a yankunan da ke fama da matsalar tsaro, inda dakarun ke cigaba da sintiri da farautar sauran ƴan bindigar da suka tsere.

Wannan na zuwa a wani lokaci da hukumomin tsaro ke ƙara zage damtse wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, musamman Katsina da ke fama da hare-haren ƴan ta’adda.

Follow Us