Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare a Jihar Katsina, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda ta ɗauki sabbin tsare-tsare na musamman da nufin farfaɗo da tsarin ilimi da kuma inganta makarantun gwamnati a faɗin jihar.
Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta musamman da Manema labarai a ofishinta da ke Babbar Sakateriyar gwamnatin jihar da ke Katsina, inda ta fayyace wasu daga cikin muhimman matakan da aka ɗauka domin sake fasalin harkar ilimi.
Sabon Tsari na "Action Plan" Don Daidaita Makomar Ilimi
A cewar Kwamishiniyar, ma’aikatar ilimi ta fitar da sabon tsarin aiki mai taken “Action Plan” wanda zai zama kundin tsarin makarantun gwamnati, inda kowacce makaranta za ta kasance cikin wannan tsari domin daidaita hanyoyin koyarwa da gudanarwa.
“Mun gano cewa kowace makaranta na aiki ne da tsarin kanta, hakan kuwa yana hana ci gaba. Wannan sabon tsari zai kawo daidaito tsakanin makarantu da malamai domin samar da inganci da kuma sauƙaƙe duba tsarin kowacce makaranta daga matakin ƙasa,” in ji ta.
Dage Koyarwa A Ramadan, da Sabon Sauyin Jadawalin Jarrabawa
Kwamishiniyar ta bayyana cewa an dage koyar da ɗalibai a dukkan makarantun gwamnati a lokacin watan Ramadan, bisa ga wata doka da gwamnatin jihar ta kafa tun a shekarar 2022. Saboda haka, zangon karatu na biyu da aka fara a watan Janairu ya kasance mai gajeren lokaci, inda aka gudanar da jarrabawar zangon bayan koma wa makaranta.
“Dokar hana koyarwa a Ramadan tana nan daram, kuma hakan ne ya sa zamu gudanar da jarrabawa nan da nan bayan dawowar ɗalibai daga hutun Ramadan,” in ji ta. Ta ƙara da cewa zango na biyu zai ci gaba da haɗuwa da zango na uku don ɗalibai su samu cikar adadin makonni da ake bukata a tsarin ilimi.
Gina Cibiyoyin Bayanai da Kaddamar da Tsarin Bincike Ta Intanet
Wani babban sauyi da Kwamishiniyar ta bayyana shi ne shigar da fasahar zamani a tsarin sa-ido da gudanar da makarantu. Ta ce gwamnati ta samar da na’urorin kwamfuta sama da 300 da za su taimaka wajen karɓar rahotanni daga kowane mataki na makarantu.
“Mun samar da tsarin intanet da za a riƙa aika rahotannin kai tsaye daga makarantu zuwa matakin ma’aikatar ba tare da amfani da takarda ba. Wannan tsari zai hana ɓoye gaskiya da almundahana, kuma zai taimaka wajen daidaita rahotanni,” kamar yadda ta bayyana.
Kwamishiniyar ta kuma sanar da cewa gwamnatin jihar ta kaddamar da sabon tsarin rajistar ɗalibai ta hanyar kwamfuta, wanda zai ba ɗalibai damar samun lambar shaida ta musamman wadda ke ɗauke da dukkan bayanan ɗalibi tun daga shekara ta ɗaya har zuwa lokacin kammala makaranta.
“Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin Katsina ta shigo da tsarin rajistar ɗalibai ta hanyar kwamfuta. Za mu samar da cikakken bayanin ɗalibi da hotonsa, jinin jikinsa, da duk wani bayani da zai taimaka wajen kula da lafiyarsa da ci gabansa a makaranta,” in ji ta.
Daga cikin sabbin shirye-shirye masu armashi, gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin “Daga Gona Zuwa Gidan Abinci” (From Farm to Kitchen), wanda zai bawa makarantu damar noma amfanin gona domin ciyar da ɗaliban da ke zaune a makarantun kwana.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa shirin zai fara aiki a wannan zangon, inda aka zaɓi makaranta ɗaya daga kowanne yanki na sanata domin fara gwaji kafin yadawa zuwa sauran makarantun gwamnati.
“Gwamnati za ta raba iri da kayan aiki ga makarantu domin su noma kayan abinci da za su ci, maimakon dogaro da abinci daga kasuwa. Wannan zai koyar da ɗalibai sana’ar noma kuma ya rage ƙudin ciyarwa,” ta bayyana.
Matsayin Cibiyar ERC Wajen Shirya Jarrabawa da Kula da Tsarin Ilimi
A ƙarshe, Kwamishiniyar ta yi bayani kan muhimmancin Cibiyar Kayayyakin Ilimi ta Jihar Katsina wato "Education Resource Center" (ERC), inda ta ce wannan cibiya ce ke da alhakin fitar da jarrabawa da kuma bin diddigin aikin koyarwa da malanta a fadin jihar.
“ERC za ta kasance cibiyar kulawa da bin sahun dukkan abubuwan da suka shafi koyarwa, shirya jarrabawa da kuma gyara tsarin ilimi a jihar,” in ji ta.