Ƙungiyar Lauyoyi Ta Kasa, NBA reshen jihar Katsina ta yi Allah-wadai da ayyukan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Katsina, KASSAROTA na cigaba da kamen baburan jama'a ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
Ƙungiyar lauyoyin ta ce babu adalci kuma akwai zalunci ƙarara a cikin kamen baburan da KASSAROTAR ke yi saboda tana kama baburan ne bisa dalili na rashin lamba, a dai dai lokacin da babu lambar a wadace kuma ana cigaba da kama jama'a ana cin su tarar kuɗaɗe
A wata hira da Alfijir Radio, shugaban ƙungiyar Lauyoyin reshen jihar Katsina, Barista Shafi'u Umar Karfi ya bayyana cewa ƙungiyar ta samu bayanai daga jama'a cewa jami'an hukumar KASSAROTA na cigaba da kama baburan jama'a kuma suna cin su tarar kudi daga Naira 10,000 zuwa 20,000 dalilin rashin Lalamba a daidai lokacin da hukumomin dake da alhakin sayarda Lambar baburan ta gaza samar da ita ga masu baburan duk da cewa sun nemi a saida masu.
Kungiyar Lauyoyin ta bayyana lamarin a matsayin takurawa ga yan kasa masu son bin doka wadanda aka gaza taimakamawa wajen kokarin cika ka'idojin dokar bin tituna da baburan su a cikin jihar ta Katsina.
Kungngiyar Lauyoyin ta bukaci Hukumar ta KASSAROTA ta dakatar da kamen baburan jama'a, a maimakon hakan ta maida hankali wajen tabbatar da cewa akwai wadatattun takardun da Lambobin baburan a wajen hukumomin da ke da alhaki kafin cigaba da kamen baburan jama'a.
Sanarwar ta kuma tunatar da cewa" KASSAROTA ta sani fa cewa ita hukuma ce da aka dora ma alhakin tabbatar da bin ka'idojin hanyoyi da na tuki, ba ta da ikon yankema Jama'a hukunci sai dai ta gurfanar dasu a kotuna bisa laifukan da suka sabawa dokokin hukumar.
"Muna kira ga Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya shiga tsakani domin tabbatar da cewa KASSAROTA ta dakatar da kamen baburan har sai an tabbatar da hukumomin dake da alhakin samar da lambobin sun wadatar dasu ga masu bukata tare da tilastama KASSAROTA ta daina sanyawa masu baburan tarar kudin da bata dace ba", Inji Kungiyar Lauyoyin.
Sai dai kuma a lokacin da hukumar kiyaye hadurran da kula da hanyoyin ta jihar Katsina, KASSAROTA take maida martani akan lamarin tace doka ta basu damar kama mutane bisa karya dokokin tuki da na hanyoyi ciki har da rashin lamba
Martanin ta wayar tarho ta bakin babban darektan hukumar Major Garba Yahayya Rimi Mai ritaya ya tabbatar da cewa suna aikin su bisa doka kuma ba babu inda dokar tace su tsaida aikinsu saboda wani bangare ya gaza cika aikinsa
Dangane da tara da suke cin masu karya dokokin hukumar, Major Rimi yace dokar hukumar ce tayi tanadin tara akan kowane laifi da ya saba dokokin hukumar, yana mai kira ga masu ababen hawan su kasance masu bin dokokin hanyoyi domin kaucema fushin hukumar tare da bada gudummuwarsu wajen kaucema hadurra a kan hanyoyin dake fadin jihar