Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar da cewa za a samu ƙarin kuɗaɗen shiga sakamakon ci gaban da aka samu a fannin tsaro a faɗin jihar.
A ranar Laraba, gwamnan ya ziyarci wasu wuraren haƙar ma'adinai a ƙananan hukumomin Anka da Maru domin duba albarkatun ƙasa da samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa ziyarar ta mai da hankali ne kan gano albarkatun ƙasa na jihar da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ma'adinai.
Ziyarar Gwamna Lawal a Kamfanin Comet Star Industry
Gwamna Lawal ya fara rangadin nasa ne da ziyartar kamfanin Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka. Kamfanin, mallakin Prince James Uduji OON, yana sarrafa kusan tan 1,000 na ma'adinai a kullum tare da amfani da sabbin fasahohin haƙa domin tabbatar da ingantaccen aiki.
Yayin da yake rangadi a masana'antar, Gwamnan ya duba wurare da dama ciki har da sassan injina, kayan aiki, da gidan wutar lantarki da ke samar da hasken lantarki ga kamfanin.
Gwamna Lawal: "Ci Gaban Tsaro Zai Haɓaka Tattalin Arziki"
Bayan kammala rangadin, Gwamna Lawal ya bayyana jin daɗinsa da yadda masana'antar ke tafiya, yana mai cewa irin wannan jarin shi ne gwamnati ke buƙata don ci gaban jihar.
"Na ji daɗi a yau domin wannan yana nuna cewa an samu ci gaba a fannin tsaro a Zamfara. Ina godiya ga sojoji da sauran masu ruwa da tsaki da suke aiki tukuru domin samar da zaman lafiya," in ji Gwamna Lawal.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jiha, da kamfanoni masu zaman kansu domin fahimtar albarkatun ƙasa da inganta su.
"Wannan jiha tana da albarkatu masu yawa, idan muka yi amfani da su yadda ya kamata, tabbas za mu bunƙasa tattalin arzikin Zamfara cikin sauri," in ji shi.
Goyon Bayan Masu Haƙar Ma’adinai a Maru
A ƙaramar Hukumar Maru, Gwamna Lawal ya yi wa masu haƙar ma'adinai alƙawarin cikakken goyon bayan gwamnati matuƙar suna aiki bisa doka.
Ya bayyana shirinsa na samar da kayan aiki masu mahimmanci don kauce wa gurɓatar muhalli, tare da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya don tabbatar da aiwatar da ƙa'idojin da suka dace.
"Zan turo Kwamishinan Muhalli domin tattaunawa da ku kan yadda za a gudanar da rajista, domin hakan zai ba mu damar taskace sahihan bayanai," in ji Gwamna Lawal.
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jiha za ta tallafa wa masu haƙar ma'adinai ta hanyar samar da takardun izini daga Gwamnatin Tarayya, amma sai sun kafa ƙungiyoyin taimakon kai da kai.