Alhaji Abdul Aziz Maituraka, daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Katsina, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaben 2027 tare da ci gaba da mulki da yardar Allah.
Maituraka ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, yayin taron sada zumunci da barka da Sallah da ya kira tare da shugabannin jam’iyyar APC da kansilolin karamar hukumar Katsina.
Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su fito fili su tallata APC ba tare da jin tsoro ko shakka ba, domin a cewarsa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ne za su ci gaba da jagoranci bayan 2027.
“Ina da ra’ayi, na fadi nawa, kuma ba na hana kowa fadin nasa,” in ji Maituraka.
Ya kara jaddada cewa shi dan jam’iyyar APC ne na kwarai kuma zai ci gaba da goyon bayanta a kowane mataki ba tare da jin tsoro ko fargaba ba. Daga karshe, ya mika kyautar goron Sallah ga shugabannin jam’iyyar da kansilolin a matsayin barka da Sallah.
A nasa jawabin, babban bako a taron, zababben Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isa Miqdad AD. Saude, ya yaba da kokarin Maituraka na ci gaba da karfafa jam’iyyar a yankin.
Hon. Miqdad ya tabbatar da biyayyarsa ga Alhaji Abdul Aziz Maituraka tare da daukar duk wata shawara da zai bayar domin ci gaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Katsina.
Daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wurin taron sun hada da Alhaji Babangida Shinkafi, Sakataren Tsare-Tsare na APC na Jihar Katsina, Shugaban APC na karamar hukumar Katsina, Alhaji Mustapha K/Bai, da Malam Gambo Dan Agaji, Shugaban jam’iyyar APC na mazabar Wakilin 2, wadanda suka jinjinawa Maituraka bisa irin kokarinsa na ci gaba da inganta jam’iyyar a jihar.