AN KAIWA ‘YAN HISBAH HARI DA BINDIGA YAYIN DA SU KE GUDANAR DA AIKINSU A KATSINA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes31032025_140750_FB_IMG_1743429270217.jpg

An kaiwa ma’aikatan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina hari da miyagun makamai da su ka hada da bindiga, ranar Asabar da kimanin karfe 2:30 na dare. Ma’aikatan Hukumar ta Hisbah sun je hana matasa yin kwallo ne a kan titi bayan da al’ummar unguwar su ka kai koke a kan yadda matasan ke takurawa masu Sallar Tahajjud, masu Bacci a gidajen unguwar da kuma amfani da hanyar.

Bayan isar jami’an na Hisbah a wurin, sai kawai matasan su ka afka masu su na jifarsu da duwatsu kafin daga baya su fito da miyagun makamai. Jami’an na Hisbah da ba su wuce kimanin su goma (10) ba, sun sanar da Hedikwatarsu yayin da su ka ga al’amarin ya fi karfinsu saboda yawan matasan da ke karuwa. An ba su umurnin su janye daga wurin wanda nan take su ka bi wannan umurni. Yayin da su ke janyewa sai su ka fahimci akwai jami’i daya da ba su gani ba a cikinsu. Domin ceto rayuwarsa sun zagaya da motarsu ta wasu lunguna domin dauko shi a inda taron matasan su ka sake zagaye su, su na jifa, duka, sara da harba bindiga.

A na cikin haka ne sai ga Alh. Sirajo Mai Asharalle ya fito da bindiga. Shugaban jami’an na Hisbah da su ka je wannan aiki, ya tarbi Alh Sirajo Mai Asharalle ya ce masa “Baba ni ma danka ne, mun dawo ne daukar dan uwanmu da mu ka bari”. Kawai taron matasan nan su ka cigaba da dukan wannan jami’i, yayin da shi kuma Mai Asharalle ya tsuguna da bindiga ya yi saiti ya harbi jami’an Hisbah da ke cikin bayan mota da kusa da ita. Nan take jami’an Hukumar ta Hisbah guda biyar (5) su ka samu miyagun raunuka.

Wadanda a ka raunata sun hada da:

1. Aminu Musa Yari
2. Ya’u Musa Ingawa
3. Kabir Abdullahi
4. Muhammad Ibrahim
5. Yunusa Saleh
6. Mustapha Isah

Hudu daga cikin wadanda su ka samu raunuka sun same su ne sakamakon harbi da bindiga, uku kuma sarar su a ka yi. Akwai shugaban tawagar wanda shi kuma ya samu ciwon kafa sakamakon duka da jifa.

An dai kai jami’an Babbar Asibitin Katsina, inda daga bisani jami’an asibitin su ka ce ba zasu iya duba su ba, su ka bada umurnin mayar da su Asibitin Koyarwa ta Tarayya da ke cikin Birnin na Katsina.

Dama dai an sha kaiwa jami’an na Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina hari a baya da yunkurin daukar rayukansu ko watanni biyu da su ka wuce an kai masu hari lokacin da suke kokarin hana BAƊALA  a ka jikkata jami’ai biyu wadanda su ka zubar da jini da yawa kuma su ka sha jinya, wanda har yanzu a na cikin binciken lamarin domin daukar matakin shari'ah.

Follow Us