BANKIN CBN DA BUKUKUWAN MUSULMI, ME YA SA AKA NUNA BANBANCI?..Binciken Musamman

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29032025_200804_CBN-Governor-Yemi-Cardoso-.jpg

@ Katsina Times 

Wani bincike da jaridun KATSINA TIMES suka gudanar, sun gano tare da tabbatarwa, a bukin Kirsimetin da ya gabata, Babban Bankin Nijeriya  (CBN), ya tabbatar da yawaitar kuɗi a bankuna, har da sabbin kuɗi domin a yi hidimar Kirsimati da sabuwar shekara cikin nasara.

Binciken da muka yi mun tabbatar CBN a lokacin har gargaɗin bankuna ya yi a kan saka kuɗi a ATM ɗinsu. Sannan da wadata bankunan da kuɗi wanda ko nawa ka je za ka iya samu.

CBN ya kuma samarwa da bankuna sabbin kuɗi daga Naira 200 zuwa Naira 5.

Amma bincikenmu a jiya Juma'a, wanda bankuna suka kulle har sai bayan Sallah an samu ƙarancin kuɗi a bankuna sosai, musamman a jihohin Musulmi. 

Mun tabbatar da wannan a jihohin Katsina, Kano, Sakkwato, Zamfara da Kebbi.

Bankuna sun riƙa ba da ƙarancin kuɗi na Naira dubu 20 ne kacal. Ko kuma mutum ya jira sai wani kwastoma ya kawo kuɗin ajiya a ba shi.

Maganar sabbin kuɗi kuwa babu maganarsu kwata-kwata. CBN bai bai wa bankuna ba, kamar yadda ta ba da lokacin bukin Kirsimeti.

Wannan bambancin yana cikin abin da muka ji ana magana a waɗannan jihohin. 

Bukin ƙaramar Sallah wato Sallah ta kammala Ramadan ita ce buki mafi girma ga Musulmi, ita ce ake hidima daban-daban bayan an buɗe baki da kammala wata guda ana Azumin watan Ramadan.

An daɗe ana zargin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Michael Cardoso da aiwatar da wasu ayyuka na nuna bambanci ga Arewa da kuma Musulmi.

Idan wannan ya fito ƙarara Allah kaɗai ya san na wa aka yi ƙarƙashin ƙasa, ko kuma nawa ake yi a ƙarƙashin ƙasa.

Mun yi duk ƙoƙarin jin ta Bakin mai magana da yawun Babban Bankin, amma ba mu yi nasara ba. 

Mun aika saƙo ta email da kuma ta wayar hannu da ta WhatsApp duk babu amsa.

Follow Us