Yana yin barci a cikinta da fatan cewa zata iya hana shi saurin tsufa kuma zata taimaka wa Michael Jackson ya yi tsawon rai.
A halin yanzu na'urar tana cikin wani sito a California, Amurka.
Michael Jackson (1958-2009) yayi amfani da wannan na'ura mai darajar dalar Amurka 100,000 (Ta Lokacin) a ƙarshen shekarun 1980s.
A lokacin Michael Jackson yakan yi barci a ciki ta. Micheal Jackson ya taba bayyana cewa lokacin da ya farka, jikinsa ya yi masa dadi kuma a ransa ya ji farin ciki, wanda ya sa ya yi fatan cewa zai iya rage tsufa da kuma rayuwa mai tsawo.
Michael Jackson ya mallaki injin nasa na kansa kuma ya kai shi gidansa na Neverland Ranch villa inda yake zaune. Ka'idar aikin wannan na'ura ita ce samar da iskar oxygen sau uku fiye da shakar iska ta al'ada, kuma a lokaci guda, kuma tana da oxygen mai tsabta. An ce wannan hanyar tana taimakawa wajen rage saurin tsufa.
Michael Jackson yayi amfani da injin samar da iskar oxygen shekaru 30 da suka gabata. A halin yanzu, ana ajiye da na'urar a wata ma'ajiya a kudancin California (Amurka) kuma mallakar wani kamfani ne na fasahar injiniyoyi.
A shekarar 1986, Michael Jackson ya fara amfani da wannan na'ura na dala 100,000 da fatan za ta taimaka masa wajen rage tsufa kuma ta haka zai taimaka masa ya yi tsawon rai.
Michael Jackson Ya Mutu a Ranar 25 ga watan Yuni 2009 yana da shekaru (50).
Daga Muhammad Cisse