Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty International, ta bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kuma da gaskiya kan kisan gilla da aka yi wa matafiya 16 a Uromi, Jihar Edo. Wadanda aka kashe mafarauta ne daga Jihar Ribas da ke kan hanyarsu zuwa Kano don bikin Sallah inda ‘yan banga da matasa dauke da makamai suka tare su, suka janye su daya bayan daya daga motarsu, suka yi musu duka sannan suka banka musu wuta. Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wadanda aka kashe ke rokon ‘yan bangan da suka kai musu dauki yayin da taron jama’a ke kallo suna ihu.
Kungiyar Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya da su dauki matakan da suka wuce yin Allah wadai kawai, su kama tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kotu. Ta gargadi gwamnati kan yadda gazawarta na hukunta irin wadannan laifuka ke karfafa gwiwar ‘yan banga da sauran kungiyoyin sa kai su dauki doka a hannunsu.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda ‘yan banga ke ci gaba da tare hanyoyi suna aikata ta’addanci ba tare da hukunta su ba. Ta soki yadda hukumomi suka gaza kawo karshen wadannan kashe-kashe na kisan gilla, inda ta bukaci a dauki kwararan matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Amnesty International ta jaddada bukatar inganta kayan aiki da horo ga ‘yan sanda domin su samu damar dakile irin wadannan hare-hare da kuma tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu. Ta ce sai an dauki matakin da ya dace kafin a dakile yaduwar irin wadannan munanan laifuka.