Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA) ta musanta zargin bacewar kudade har Naira miliyan 407 a asusunta, kamar yadda wata kafar labarai ta yanar gizo ta wallafa, bisa wani rahoto da ofishin Mai Binciken Kudi na Jihar ya fitar.
A wata sanarwa da ta fito daga hukumar, mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a, Musa Sa’idu, KTSTA ta bayyana cewa badakalar kudaden da ake magana akai ta faru ne tun a shekarar 2016, kafin a nada sabbin shugabannin hukumar.
"Kudaden da aka kashe ba bisa ka’ida ba, har Naira miliyan 407, da kuma Naira miliyan 24 na kudaden shiga da ba a san inda aka kai su ba, sun kasance a cikin rahoton binciken. Daga karshe, an umarci wadanda ke da alhakin tattara kudaden su mayar da su a asusun hukumar," in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, an nada Haruna Musa Rugoji a matsayin Shugaban KTSTA a shekarar 2018, bayan sauyin wurin aiki da aka yi masa tare da Hon. Babangida Nasamu. Tun bayan nadinsa, ba a samu rahoton wata badakalar kudi ba a hukumar.
Sanarwar ta kara da cewa lokacin da Haruna Musa Rugoji ya karbi ragamar hukumar, ya gaji bashin sama da Naira miliyan 50, wanda ya biya duka. "Basussukan sun hada da albashi da alawus na ma’aikata, da bashi daga dillalan motocin, kanikawa, da masu sayar da kayan motoci," in ji sanarwar.
Dangane da kayan aiki, hukumar ta gaji motoci 106, amma guda 57 ne kawai ke aiki. Yanzu, duk motocin KTSTA suna aiki kuma suna samar da kudaden shiga ga gwamnatin jihar.
Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa shugabancin KTSTA na yanzu ya bullo da tsarin hadin gwiwa da masu zaman kansu, wanda ya kara samar da kudaden shiga ga hukumar. "A yau, KTSTA tana tafiyar da budadden asusu, inda duk abin da ake samu a bayyane yake, kuma gwamnati na sane da yadda ake tafiyar da kudaden."
Hukumar ta ce tana aiki kafada da kafada da gwamnatin Malam Dikko Umar Radda wajen tafiyar da asusunta bisa tsantseni da gujewa almundahana. Cikin kudaden da take samu, har ta fara gina sabbin tashoshi a wasu sassan jihar domin saukaka zirga-zirga ga matafiya.
A karshe, KTSTA ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da asusunta, tare da inganta harkokin sufuri a Jihar Katsina.