Kamar yadda ya saba a duk shekara a cikin wata Ramadan, jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, na nuna karimcinsa ta hanyar raba fakejin abinci, wanda aka fi sani da ‘Iftar Hadiyya,’ ga mabuƙata.
Kamar yadda ya saba a wannan karon an gudanar da rabon ne a Suleja (a jihar Neja), Maraba (a jihar Nasarawa), Kuje har zuwa ga mazauna babban birnin tarayya da kuma yankunan da ke maƙwabtaka da su.
Wannan shiri na da nufin sauƙaƙa wa masu azumi nauyi tare da bayar da tallafin da ake buƙata a cikin watan Ramadan.
Daraktan ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky, Malam Hassan Bala ne ya bayyana shirin a lokacin rabon kayayyakin abincin.
Sama da shekaru 30 ke nan, Shaikh Zakzaky na ci gaba da tabbatar da wannan aikin na alheri, tare da tabbatar da cewa al’umma da dama za su iya buɗa baki cikin sauki.
A farkon wannan wata na Ramadan, idan ba ku manta ba, ya bayar da irin wannan tallafi ga al’ummar Zariya da kewaye, da ma sauran jihohin ƙasar nan.
Waɗanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun nuna matuƙar jin daɗinsu ga Shaikh Zakzaky bisa yadda yake nuna goyonsa bayan sa ga mabuƙata ta hanyar ba su tallafi, tare da yi masa addu’o’in samun cikakkken ƙoshin lafiya.
Wannan al’adar ta ‘Iftar Hadiyya’ ta kasance wata ɗabi’a ce ta sadaukarwa da Shaikh Zakzaky ke yi ga ayyukan jin ƙai, kuma ana sa ran wannan aiki zai ci gaba da gudana a shekaru masu zuwa.