Kungiyar masu zana gidaje ta kasa reshen jihar Katsina, wato The Nigerian Institute of Architects (NIA) Katsina State Chapter, ta shirya taron shan ruwa (Iftar) ga membobinta domin karfafa zumunci da hada kai a tsakaninsu.
Taron wanda aka gudanar a sakatariyar kungiyar da ke tsohuwar ma’aikatar Works ta jihar Katsina, a ranar Lahadi, 23 ga Maris, 2025, ya samu halartar membobin kungiyar, gamayyar wasu kungiyoyin da ke da alaka da fannin gine-gine, da kuma injiniyoyi daga sassa daban-daban.
Da yake jawabi a yayin taron, shugaban kungiyar a jihar Katsina, Architect Kamaluddeen Dahiru FNIA, RARCON, RTC, ya bayyana cewa wannan taron na Iftar wata al’ada ce da suka saba gudanarwa a duk shekara tun daga shekarar 2012, domin sada zumunci da karfafa hadin gwiwa a tsakanin ‘yan uwansu da ke harkar gine-gine.
Ya jaddada muhimmancin hadin kai da bayar da gudunmawa wajen bunkasa aikin su da kuma habaka ginin birane da yankunan karkara a jihar Katsina da Najeriya baki daya.
Arc. Kamaluddeen ya kuma yi kira ga membobin kungiyar da su kara kaimi wajen inganta ayyukansu da kuma taimakon juna, yana mai cewa hakan ne kadai zai tabbatar da ci gaban wannan sana’a da kuma dorewar ingancinta a jihar.
Bugu da kari, shugaban ya yaba da kokarin Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, bisa daukar nauyin taron, inda ya bayyana hakan a matsayin wata gagarumar gudunmawa ga kungiyar.
Baya ga haka, Arc. Kamaluddeen ya mika sakon ta’aziyyar kungiyar ga Gwamnan Jihar Katsina bisa rasuwar mahaifiyarsa, yana mai addu’ar Allah ya jikanta da rahama.
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a taron sun hada da: Arc. Abdussalam, Arc. Abdulmajid Salihu, Muntari Sani (Sarkin Yamman Daura), Mustapha Maikudi Kankia (Dujiman Kankiya), Injiniya Abbas Sada Sani, da sauransu.
An ci an sha, an tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gaban sana’ar gine-gine, tare da rarraba Alkur’ani da wasu littafai da aka tarjama zuwa harshen Turanci da Hausa domin karfafawa membobin kungiyar da sauran mahalarta gwiwa.
Taron ya gudana cikin nasara, inda mahalarta suka jinjinawa irin wannan yunkuri na kungiyar da kuma bukatar ci gaba da irin wadannan taruka domin cusa kwarewa da bunkasa sana’a a tsakanin ‘yan uwansu masu zana gidaje.