Dan Majalisar Tarayya a Katsina Ya Kara Alawus Ga Limamai da Ladanai a Yankinsa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22032025_194133_FB_IMG_1742672393471.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

A kokarinsa na tallafawa shugabannin addini da ke kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Aminu Balele Dan’arewa, ya sanar da karin alawus ga Limamai, Na’ibai, da Ladanai a yankin. Wannan mataki ya zo ne domin saukaka musu da kuma kara jin dadin ayyukansu a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar rayuwa.

Tun farko, Dan’arewa yana bawa kowanne Limami N10,000, Na’ibi N8,000, sai Ladani N5,000 a kowane wata. Sai dai, da yake la’akari da halin da ake ciki, yanzu ya kara alawus din zuwa N15,000 ga Limamai, N12,000 ga Na’ibai, sai N10,000 ga Ladanai, wanda hakan ke nufin karuwar kaso mai yawa daga abin da ake biya a baya.

Da yake jawabi a madadin Dan Majalisar, Shugaban Karamar Hukumar Kurfi, Dakta Mannir Shehu Wurma, ya bayyana cewa Hon. Dan’arewa ya dauki wannan mataki ne domin rage wa shugabannin addini radadin halin da ake ciki. Ya ce tun lokacin da ya hau kujerar wakilci, ya dauki alkawarin tallafawa su, don haka wannan kari wani bangare ne na cikawa.

“Wannan shiri ba zai tsaya nan ba, zai ci gaba har zuwa karshen wa’adinsa a majalisa. Hakan na daga cikin kokarinsa na inganta walwalar shugabannin addini a yankinsa,” in ji Dakta Wurma.

An kaddamar da shirin a garin Dutsinma a safiyar ranar Asabar, 22 ga Maris, 2025, inda Limamai da Na’ibai fiye da 200 suka amfana. Daga nan aka kammala shirin a Kurfi, a harabar gidan Dan Majalisar, inda ya roki limaman da su ci gaba da yi wa yankinsu da jihar Katsina addu’ar zaman lafiya da cigaba, tare da fatan nasara ga gwamnatin Malam Dikko Umar Radda.

Follow Us