Katsina Times
Shahararren ɗan wasan kwaikwayo kuma mai ƙirƙirar abun dariya, Debo Adedayo, wanda aka fi sani da Mr Macaroni, ya bayyana yadda ya faɗa cikin matsalar kuɗi da ta kai shi ga bashin Naira miliyan 500.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, jarumin ya bayyana cewa ya rasa dukiyar da ya tara a shekarar 2021 sakamakon zamba da kuma asarar jari, lamarin da ya sa dole ya fara ciwo bashi don biyan bukatunsa.
"Shekarun 2021/2022 sun kasance mafi wahala a rayuwata. Na faɗa tarkon zamba, kuma na yi asarar jari. A lokacin, na rasa duk abin da na tara, amma ban sanar da kowa ba," in ji shi.
Ya bayyana cewa sakaci wajen sarrafa kuɗi da yawan bayar da tallafi sun tsananta matsalarsa. Ya ce ya ciwo bashi daga wurare da dama, lamarin da ya jefa shi cikin wahala saboda tsaurara ribar ruwa.
"Ina samun miliyoyin kuɗi, don haka ban taɓa tunanin cewa bashi zai zama matsala ba. Amma sai da lokaci ya kure min kafin na fahimci cewa ribar da nake samu na tafiya ne wajen biyan ruwa," in ji shi.
Ya bayyana shekarar 2024 a matsayin lokaci mafi wahala a rayuwarsa, domin har yanzu yana fuskantar basussuka da suka kai rabin biliyan. Har ila yau, ya nuna takaicinsa kan cin amana da ya fuskanta daga mutumin da ya ɗauka a matsayin "aboki da 'yar'uwa."
Sai dai, Mr Macaroni ya nuna godiya ga iyalansa da abokansa da suka tsaya masa a wannan mawuyacin hali. Ya ce a yanzu yana jin daɗin rayuwa fiye da shekaru uku da suka gabata.
A ƙarshe, ya gargaɗi masoyansa kan cin bashi, yana mai ba su shawarar su kasance masu sarrafa kuɗinsu cikin hikima.
"Don Allah, kada ku ciwo bashi! Amma idan dole ne, to ku kasance masu kula," in ji shi.