Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile yunƙurin ƴan bindiga na garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar.
Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴansandan, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya baiwa Alfijir Radio ta bayyana cewa lamarin ya faru ne jiya Laraba a lokacin da ƴanbindigar ɗauke da muggan makaman AK-47 kan babura suka yi yunƙurin tare ƙaramar hanyar Inono zuwa ƙauyen Gidan Zuma a ƙaramar hukumar Sabuwa domin garkuwa da matafiya.
Sai dai DPOn ƴansandan ƙaramar hukumar Faskari bai yi wata-wata ba ya haɗa tawagar jami'an sa suka garzaya wurin suka yi musayar wuta da ƴanbindigar wanda ya tilasta musu tserewa da raunukan harbin bindiga jikinsu, tare da barin babur ɗaya ƙirar Honda wanda ƴansandan suka taho da shi.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar na yunƙurin ganin ta cafke maharan da suka tsere yayin da jami'an su suka yiwa yankin ƙawanya.
Kwamishinan ƴansandan jihar Katsina ya yabawa jarumtar jami'an bisa ɗaukar matakin gaggawa wanda ya nuna ƙwazon su na kare rayuka da duniyoyin al'ummar jihar.
Rundunar ta kuma sanar da cewa za ta fitar da ƙarin bayani nan gaba yayin da ta ke cigaba da gudanar da bincike.
Katsina Police Command