Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda a Kankara – Dr. Nasir Mu’azu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19032025_225132_IMG-20250319-WA0267.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times.
Katsina Nijeriya, 18 Ga Maris 2025 – 

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta sanar da nasarar atisayen hadin gwiwa da dakarun Brigade ta 17 tare da hadin gwiwar Rundunar Sojin Sama ta Operation Forest Sanity, wanda ya kai ga kubutar da mutane 84 daga hannun ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Kankara.

A cewar Dr. Nasir Mu’azu, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida, atisayen ya fara ne da misalin karfe 09:00 na safe, inda jami’an tsaro suka kaddamar da farmaki a maboyar fitaccen dan ta’adda, Sanusi Dutsin-Ma, da ke tsaunukan Pauwa a Kankara. Atisayen ya kunshi hare-haren sama da kuma farmakin kasa daga dakarun soji, wanda ya kai ga fatattakar ‘yan ta’adda.

“A yayin aikin, jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka fatattake su zuwa cikin tsaunuka. Da misalin karfe 15:09, dakarun tsaro sun isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, inda suka fafata da ‘yan ta’adda har zuwa karfe 16:30 na yamma. A sakamakon haka, an hallaka ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu suka tsere da raunuka,” in ji Dr. Nasir Mu’azu.

Kwamishinan ya ce, jami’an tsaro sun ceto mutane 84 da suka hada da maza 7, mata 23, da yara 54 da aka yi garkuwa da su. Haka kuma, an lalata wasu kayayyakin da ake zargi, ciki har da kakin soja da wasu abubuwa masu hadari.

“An bai wa mutanen da aka ceto abinci da kulawar gaggawa kafin mika su ga hukumomin kananan hukumomi don ci gaba da kula da su tare da hadewa da iyalansu,” in ji shi.

Gwamnati ta yabawa kwazon jami’an tsaro da suka kammala wannan aiki ba tare da asarar rai daga bangaren gwamnati ba.

“Wannan nasara wata alama ce ta jajircewar Gwamnatin Jihar Katsina a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro. Kubutar da wadannan bayin Allah, musamman yara kanana, yana nuna irin kudirin Gwamna Dikko Umaru Radda na tabbatar da tsaro a jihar,” in ji Dr. Mu’azu.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya domin kawar da miyagun laifuka tare da tabbatar da tsaro ga dukkan mazauna jihar.

Follow Us