Daga Kundin Danjarida Na Shekarar 2003
Na isa Otal ɗin NICON a ranar yara (Children’s Day). Ba da kudina na biya ɗaki ba, gayyata ce ta kai ni wani taro. Da na shiga, sai na sauke ajiyar zuciya, na ce yau fa karyar Dan Afantama ta kare. Haka aka biya min kuɗin ɗaki zunzurutu har N25,000, muka hau lif ɗin da ya kai mu hawa na bakwai. Ashe, tsiya mai lasi na cikin daki!
A cikin ɗakin akwai ƙaramin firji da aka ajiye kayan shaye-shaye iri daban-daban. Bari ku ji! Akwai kwalbar robar ruwan Yankari da ake sayarwa N70 a Kano, amma a NICON farashinta ya kai N500. Kwalbar Koka-Kola kuwa ana sayar da ita N350.
Allah da ikonsa, cikin dare bayan mun gama sharɓar romo iri-iri, sai wani daga cikin abokan tafiyata ya ji jiki da gudawa. An nemi agajin gaggawa, muka rutsa zuwa wani shagon magani a cikin otal ɗin. Muka nemi Buscopan da Flagyl, waɗanda kudinsu a kasuwa ba ya wuce N40. Amma sai ga wata mace ta fito da rasidi, ta rubuta N3,000.
Da na ga abin ya fi ƙarfin fahimtata, sai na fara magana da Turanci, wai ni ba zan biya haka ba, idan ba ta yarda ba, ta karɓi N50 kawai ko kuma ta bar maganin. Ashe ita ma ta yi shirin faɗa, sai ta ce da ni da “broken English”, "See me trouble! If una no get money, wey una spend enjo, why una carry yeye leg come from village? Abi dis place na bush?"
Ba mu da wata mafita, dole wani baturen da ya gayyace mu ya fiddo kuɗin ya biya.
Kuɗaɗen Tsiya a Otal
Wata mata da ta zo tare da ɗan ta mai shekara uku ta ɗan fita waje. Kafin ta dawo, sai ga yaro ya shanye ƙaramin kwalin lemon Five Alive wanda ake sayarwa N100 a kasuwa. Ashe a otal ɗin, farashinsa N900 ne! Sai da ta biya.
Ni ma dai, wai ga dan gaye, na ɗauki chocolate daga firji ina ci, ina shan iska ina kallon talabijin. Na shanye guda huɗu! Na tabbatar idan saya zan yi a Zango Stores da ke Kano, kudinsu ba zai wuce N280 ba. Amma a nan sai aka nuna min rasidin N2,800! Da yake ba ni da ko kwabo, dole aka cire kuɗin daga kudin sallama ta.
Kudin Kiran Wayar Gaisuwa
Za ku yi dariya idan na gaya muku wata. Wani abokin tafiyarmu ya kira wayar Kaduna don yin gaisuwa. Minti tara kacal ya yi, ya kuwa kwanta barci. Washe gari sai aka miƙa masa rasidin N6,400! Muna ta dariya, shi kuma yana rantse-rantse wai gaisuwa kawai ya yi. To kun ga dai inda ake yin gaisuwar N6,400!
Daren Tashin Hankali
Misalin ƙarfe 12:00 na dare, sai na fara jin kida na tashi a cikin otal ɗin. Abokina ya ce ba zai je ba, amma ni na nace sai na je, ko don jin labari.
Ina shiga sai na ga wani katafaren ɗaki da ba a zata irin manyan mutane su shiga irin wannan wuri ba. Amma fa sai ga su nan! Ba kunya, ba tsoron Allah, an zagaye tebura ana kwankwadar giya, ga kuma wata yarinya ko mata ce ta yi tsirara tana rawa a gaban wani.
Na ga wani hamshakin attajiri yana zaune da rangaji. Yarinyar nan ta matsa kusa da shi, sai ya sa gindin kwalbar giya ya zungure ta. Na tsaya na yi tunani: Yanzu waɗannan mutanen da ke sheƙe ayarsu a nan, idan sun koma gida, me za su ce wa matansu?
Darasi a Daren Karuwa
Abin mamaki a NICON dai ba ya ƙarewa! Na fahimci cewa, duk kyawon karuwa, idan ta kasa samun wanda zai saya ta a dare, to darajarta ta faɗi. A wannan dare, wasu karuwai har 60 suka kwana a waje saboda ba su samu masu saya ba. Ga shi kuma an yi ruwan sama, baki da yawa sun shige ɗaki don barci. Wasu ba don tsoron Allah ba, sai don gudun kamuwa da cutar zamani.
Kudin Kallo a Talabijin
Ban fa gaya muku ba, a cikin ɗakin otal ɗin akwai tashoshin talabijin da ba a yarda ka kalla sai ka biya. Idan mutum na son kallon fim guda ɗaya, dole sai ya biya N1,500. Kai, wannan shegantalka da me ta yi kama?!
Ƙarshe
An bada labarin Danjarida a Mujallar Matasa ta Watan Nuwamba 2003.