Sarkin Makafin Katsina Ya Nada Amb. Khadija Saulawa a Matsayin Sarauniyar Yaƙin Masu Bukata ta Musamman

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19032025_185248_FB_IMG_1742410154691.jpg


Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times

Sarkin Makafi na Jihar Katsina, Alhaji Garba Muhammad Nahuta, ya nada Mataimakiyar Shugaban Majalisar Matasa ta Ƙasa reshen Jihar Katsina, Amb. Khadija Suleman Saulawa, a matsayin Sarauniyar Yaƙin Masu Bukata ta Musamman. An gudanar da wannan nadin ne yayin wata ziyarar da ta kai masa a fadarsa da ke unguwar Yari, a ranar Laraba, 19 ga watan Maris, 2025.

Amb. Khadija Suleman Saulawa na ci gaba da kai ziyara ga shugabannin al'umma da malamai domin neman shawarwari kan kudurorin da take son cimmawa, musamman wajen ƙarfafa haɗin kai da inganta rayuwar jama’a, tare da samar da sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.

A yayin wannan ziyara, Sarkin Makafi da majalisarsa sun bayyana damuwarsu kan yadda har yanzu ba a samar da hukuma ta musamman da za ta kula da hakkoki da jin daɗin masu bukata ta musamman ba (Disable Commission). Sun bayyana cewa tun zamanin tsohon Gwamna, Alhaji Aminu Bello Masari, suke ƙoƙarin ganin an kafa wannan hukuma amma har yanzu ba a samu nasara ba. Don haka, suka roƙi Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda da ta duba ƙudurin, domin tabbatar da kafa hukumar da za ta inganta rayuwar masu bukata ta musamman a jihar Katsina.

A martaninta, Saulawa ta nuna damuwa kan halin da suke ciki, tare da tabbatar da cewa za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an samu kafa wannan hukuma ta hanyar amfani da duk hanyoyin da suka dace.

Baya ga haka, Saulawa ta kuma kai ziyara ga fitaccen malami, Sheikh Isma’il Zakariyya Alkashnawiy, domin neman shawarwari. Malamin ya tarbi tawagarta hannu bibbiyu, inda ya yaba da ƙoƙarinta tare da ba ta shawarwari kan yadda za ta gudanar da shugabancinta cikin hikima da jajircewa. Ya kuma yi mata ƙarin haske kan hanyoyin da za a bi wajen inganta rayuwar masu bukata ta musamman da ƙara kawo ci gaba a tsakanin al’umma gaba ɗaya.

Nadin da aka yi wa Saulawa yana nuna irin gagarumar gudunmawar da take bayarwa ga al’umma, tare da ƙarfafa masu bukata ta musamman domin samun daidaito, ingantaccen rayuwa, da ci gaba a cikin al’umma.

Follow Us