Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Katsina, Najeriya – 19 ga Maris, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin musamman domin duba tsarin karatun almajirai tare da bullo da sabbin hanyoyin inganta iliminsu da jin daɗinsu. An kaddamar da kwamitin ne a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar (SGS), inda ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD.
A yayin kaddamar da kwamitin, Sakataren Gwamnati, Abdullahi Garba Faskari, ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da inganta ilimi, musamman ta hanyar daidaita tsarin karatun almajirai da na zamani. Ya bayyana cewa kwamitin zai mayar da hankali wajen nazarin matsalolin da almajirai ke fuskanta da kuma bayar da shawarwari masu inganci don kyautata karatunsu.