Daga Danjuma Katsina | Mujallar Matasa 2009 - 2010
Kungiyoyin asiri da ke juya al'amuran duniya ba sa daukar kowa sai dai wadanda suka fito daga Amurka ko kasashen Turai. Tasirinsu ya fi shafar masu kudi da kuma shugabannin cibiyoyin kudi. Dokar farko na shigarsu ita ce a kafa su a shekarar 1915, tare da hada sojoji da masana da ke tsara yadda za a bi wajen aiwatar da wasu al'amura.
Wannan kungiya ce da ta tsara yadda za a kafa Kungiyar Gamayyar Kasashen Duniya, wadda daga baya ta rikide ta zama Majalisar Dinkin Duniya (UN).
Wannan kungiya an kafa ta ne a shekarar 1918, karkashin jagorancin Elihu Root, tsohon Sakataren Harkokin Cikin Gida a zamanin mulkin Theodore Roosevelt. Babban muradinta shi ne samar da tsarin diflomasiyya da zaman lafiya na duniya.
Wannan kungiya ce da ta horas da shugabannin Amurka, ciki har da Jimmy Carter, Bill Clinton da Ronald Reagan. A shekarar 1992, wani dan jarida mai wallafa wata jarida ya fallasa yadda kungiyar ke shiryawa da tasiri a harkokin mulkin duniya.
Wata kungiya ta sirri da ta janyo cece-kuce a Najeriya ita ce "Ogbani Fraternity". Wani dan jarida mai suna Chris Okoli ne ya yi bincike kan kungiyar tare da wallafa sunayen wasu manyan 'ya'yanta. Wannan bayani ya girgiza gwamnati da masu mulki a wancan lokaci.
Ba a shiga cikinsu sai idan sun ga kana da tasiri. Wasu daga cikin sunayen da aka bayyana a cikin binciken sun hada da:
A lokacin, wadannan shugabanni sun fito sun karyata kasancewarsu 'yan kungiya, har ma suka kai karar lamarin kotu. Bayan haka, mujallar Newbreed da ta wallafa wannan bincike ta mutu, ana zargin 'yan kungiyoyin sirrin ne suka yi yunkurin kawar da ita. Marubucin binciken, Chris Okoli, shima daga baya ya mutu cikin yanayi mai cike da shakku.
Wadannan manyan kungiyoyi na duniya ana alakanta su da wasu cibiyoyi a kasar Isra'ila, kuma ana danganta su da kungiyoyin asirin Yahudawa da ke sarrafa al'amuran duniya. Ana yi musu kallon kamar "Yajuj da Majuj", domin suna da ikon mamaye komai, suna aikinsu da tsare-tsaren su kamar Dujjal.
Duk wanda ya yarda da su ko ya kasance cikinsu, duniya tana wadata da shi, domin suna amfani da kowane irin salo don cimma manufofinsu. Abin da kawai ke ci musu tuwo a kwarya shi ne rashin samun nasarar abin da suka sanya gaba.
"Allah tsare mu daga gare su, amin."
Danjuma Katsina, Marubuci a Jaridar Almizan
Fans
Fans
Fans
Fans