Daga Danjuma Katsina
(Cigaba daga rubutun ranar Juma’a, 14 ga watan Maris, 2025)
Daga Mujallar Matasa Shekarar 2019 - 2012
A wannan rubutu, ina son kawo manyan mutane da ke juya siyasar kafircin duniya a yanzu, tare da kakanninsu da suka kafa tushen siyasar Turai.
A bincikena, na dogara ne kan wasu muhimman rubuce-rubuce guda hudu daga kungiyoyi daban-daban.
1. Littafin "Who Really Runs The World?"
Littafin farko da na karanta an rubuta shi a shekarar 2005, mai taken Who Really Runs The World? wanda Them Burneet Land ya wallafa. Ma’anar taken littafin shi ne “Su Wa Ke Juya Akalar Duniya?” Wannan littafi ya bayyana cewa ‘yan kungiyar asiri ta Skull and Bones ne suka wallafa shi, inda suka bayyana manufofinsu da kudurorinsu, tare da kare kansu daga zarge-zargen da ake yi masu.
2. Littafin "Freemasons: The Inside The World's Oldest Secret Society!"
Littafi na biyu mai suna Freemasons: The Inside The World’s Oldest Secret Society! wanda Paul Jeffers ya rubuta, ya bayyana tarihin kungiyar asiri ta Freemasons. A cikin littafin, marubucin—wanda shi ma memba ne na kungiyar—ya bayyana yadda aka kafa kungiyar, tarihinta, da yadda ‘ya’yanta ke gudanar da ayyukansu.
3. Rubutun Mujallar "New Africa"
Rubutu na uku kuwa yana cikin mujallar New Africa da aka wallafa a ranar 7 ga Fabrairu, 2008. Rubutun yana dauke da babban taken "Secret Societies: The Way Forward for Africa" (Kungiyoyin Asiri: Hanyar Da Zai Kawo Cigaba Ga Afrika). Wannan rubutu ya nuna cewa irin wadannan kungiyoyi su ne tushen cigaban kasashen Turai, inda marubutan suka jaddada cewa Afrika ma na bukatar irin wannan tsarin domin samun cigaba.
4. Rubutun Mujallar "Newswatch"
Rubutu na hudu kuma an wallafa shi a mujallar Newswatch a ranar 24 ga Nuwamba, 2008, mai taken "The Secret Society That Rules The World" (Kungiyar Asiri da Ke Mulkin Duniya). A cikin rubutun, an yi cikakken bayani kan kungiyar asiri ta Freemasons, tare da yin hira da wani jami’inta daga Najeriya, wanda ya bayyana cewa kungiyar ta sauya salonta, yanzu suna bayyana kansu domin kare martabarsu daga zarge-zarge.
Muhimmancin Wadannan Rubuce-rubuce
Dukkanin wadannan rubuce-rubuce da na ci karo da su sun tabbatar da cewa kungiyoyin asiri ne suka dauki nauyin wallafa su domin kare kansu da kuma bayyana manufarsu ga duniya.
A wannan rubutu, zan bar wasu kalmomin Turanci kamar yadda na same su a cikin littattafan domin saukaka fahimta ga masu karatu.
1. Freemasons – Kungiyar Asiri da Tafi Tasiri a Duniya
Kungiyar asiri mafi girma da tasiri a duniya ita ce Freemasons. Ita ce kuma kungiyar da tafi dadewa, tana da mambobi sama da miliyan daya da digo daya (1.1 million) a Amurka da Ingila.
Shahararrun ‘Ya’yan Freemasons:
George Washington – Mutumin da ya jagoranci yancin Amurka.
Tsohon Firaministan Birtaniya, Tony Blair.
Shugabannin Amurka da dama daga cikin mutum 56 da suka sa hannu a takardar ‘yancin Amurka, 12 cikinsu dukkansu ‘yan Freemasons ne.
Shugaban Nijar na yanzu, Mamadou Tandja.
Manyan attajirai, masana, da shugabannin kasashen duniya.
Alamun wannan kungiya na nan a muhimman wurare kamar:
Fadar White House – Babban gidan gwamnatin Amurka.
Dala ta Amurka – Alamun Freemasons na cikin tsarinta.
Kungiyar Freemasons na da rassa a kasashe da dama, kuma suna da tasiri a harkokin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewar duniya.
Wadannan bayanai sun bayyana yadda wasu kungiyoyin asiri ke taka rawa wajen juya siyasar duniya, tun daga kasashen Turai har zuwa nahiyar Afrika. A yayin da wasu ke ganin wadannan kungiyoyi a matsayin tushen cigaba, wasu kuma na kallonsu a matsayin masu kokarin mallake duniya aboye