Jami’an Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA), reshen Malumfashi, sun cafke wani da ake zargi da Satar Babur.
Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne da misalin karfe 5:00 na yamma, ranar Asabar, 15 ga Maris, 2025, yayin da jami’an KASSAROTA ke gudanar da sintiri a Malumfashi, karkashin jagorancin Aminu Sani Shargalle.
Rahotanni sun nuna cewa tun daga Zariya aka fara bin diddigin wanda ake zargin, inda ya bi ta Kano har zuwa Malumfashi da nufin batar da babur ɗin da ake zargi da satar sa. Da isarsa Malumfashi, jami’an KASSAROTA da ke sintiri suka dakatar da shi don bincike, inda suka gano cewa babur ɗin na ɗauke da lambar rajista ta bogi kuma ba nasa ba ne.
Bayan zurfafa bincike, an ci tarar wanda ake zargin kan amfani da lambar bogi, sannan aka mika shi hannun ‘yan sandan Najeriya. Daga bisani, an tabbatar da cewa babur ɗin da ke hannunsa na sata ne.
Shugaban Hukumar KASSAROTA na Jihar Katsina, Manjo Garba Yahaya Rimi (mai murabus), ya yaba da jajircewar jami’an hukumar wajen damke wanda ake zargi tare da mika shi ga hukumomin da suka dace.
Ya kuma gargadi jama’a da su guji amfani da ababen hawa da ba su da ingantacciyar rajista ko kuma ke ɗauke da lambobi na bogi. Bugu da ƙari, ya bukaci al’ummar jihar Katsina da su ci gaba da ba da hadin kai ga KASSAROTA don tabbatar da doka da oda a harkokin zirga-zirga.