Muhammad Ali Hafiziy | Katsina Times
Majalisar Matasan Najeriya (NYCN), reshen Jihar Katsina, ta kuduri aniyar kawo sauyi a cikin al’umma tare da tabbatar da hadin kai a tsakaninsu. Wannan mataki ya biyo bayan nadin sabbin shugabanni, inda mataimakiyar shugabar majalisar, Amb. Khadija Suleman Saulawa, ta fara gudanar da ziyarce-ziyarce domin kulla dangantaka da mabiya addinai daban-daban a jihar.
A ranar Lahadi, 16 ga Maris, 2025, Saulawa ta ziyarci cocin Angelican tare da ganawa da kungiyoyin matasa na Kirista, inda ta gabatar da manufofinta na hadin kai da inganta zaman lafiya tsakanin al’umma. Ta bayyana cewa burinta shi ne tabbatar da ci gaban matasa ta hanyar samar da hanyoyin inganta rayuwarsu da kuma kauce wa aikata miyagun laifuka, musamman shaye-shaye da wasu dabi’u marasa kyau.
Baya ga wannan, Saulawa ta kai ziyara ga Sheikh Yakub Yahya, wakilin Sheikh Ibrahim Zakzaky a Katsina, domin neman shawarwari da bayyana kudurorinta na samar da daidaito a tsakanin al’umma. Shehin malamin ya yi na’am da wannan yunkuri, inda ya tunatar da matasa cewa su ne jagororin al’umma, don haka dole su rungumi hakikanin ci gaba da hadin kai domin nasarar rayuwa.
A cewar Sheikh Yahya, babu wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da hadin kai da juna ba, don haka yana da matukar muhimmanci matasa su tashi tsaye wajen kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.
Shugabannin matasan Kirista da suka halarci taron sun nuna jin dadinsu da wannan ziyarar, suna mai bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da wata kungiya daga bangaren musulmai ta kawo irin wannan ziyara domin kulla dangantaka da su. Sun bayyana cewa wannan mataki ne da zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban a Jihar Katsina.
Majalisar matasan ta NYCN na da burin aiwatar da shirye-shirye na hadin kai da ci gaban matasa, tare da fadakar da su kan muhimmancin zaman lafiya da kauce wa ayyukan da ka iya kawo cikas ga ci gaban su da na al’ummarsu gaba daya.