Sule Lamido: El-Rufai da Mabiyansa Ba Za Su Iya Kayar da Tinubu Ba

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16032025_101810_FB_IMG_1742119925228.jpg


Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa Nasir El-Rufai da mabiyansa ba za su iya kayar da Shugaba Bola Tinubu ba, domin ba kishin kasa suka sa a gaba ba.

Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce shugabanci ba a yin sa da fushi, haushi ko son zuciya, sai dai da hakuri da hangen nesa.

Shugabanci Ba a Yin Sa da Fushi – Lamido

Tsohon gwamnan ya ce, "Idan ka ce za ka yi amfani da fushinka don cimma wata manufa, ba za ka taba yanke hukunci kan gaskiya ba, sai dai don son ranka."

Ya kara da cewa shugabanci yana bukatar adalci da kishin kasa, ba wai son zuciya ba. A cewarsa, "Abin da ya dace shi ne a mayar da hankali kan ci gaban kasa, maimakon nuna fushi da wata mutum ko wata kungiya."

Lamido ya ce Najeriya tana bukatar shugabanni masu kishin kasa, wadanda za su yi tafiya domin nuna cewa kasar na tafiya a kan turba madaidaiciya, ba wai a dinga nuna fushi da tayar da rikici ba.

Lamido Ya Yi Kakkausar Suka Ga El-Rufai

Lamido ya caccaki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa jita-jitar da ake yi na cewa ya fice daga jam’iyyar APC sakamakon rashin samun mukamin minista a gwamnatin Tinubu.

Bugu da kari, Lamido ya mayar da martani kan gayyatar da El-Rufai ke yiwa wasu ’yan siyasa da su fice daga PDP su shiga sabuwar jam’iyyarsa ta SDP. Ya ce, "Babu abin da Malam Nasiru ya samu a rayuwar siyasa ba tare da albarkacin PDP ba, amma ya juya ya bar jam’iyyar. Yanzu kuma yana kira ga wasu su bar PDP kamar yadda ya yi."

Tsohon gwamnan ya nuna mamakinsa kan yadda El-Rufai ke kokarin girmama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, duk kuwa da cewa a baya ya rika sukar dattawan Arewa yana cewa babu dattijo a yankin.

Follow Us