ƘUNGIYOYIN ASIRI: WANDAKE JUYA DUNIYA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15032025_085210_FB_IMG_1742028579525.jpg



Danjuma Katsina | Katsina Times 

Kungiyoyin asiri na da mambobinsu a sassa daban-daban na duniya, kuma sun samu nasarar mamaye cibiyoyin kasuwanci da mulki, musamman a ƙasashen Yamma. A yau, su ne ke da iko da akalar duniya. Sanin hakan yana da matukar muhimmanci ga mutum domin ya fahimci halin da yake ciki, tare da neman kusanci da Allah don samun kariya daga wadannan miyagun.

A baya, ana daukar labarin wadannan kungiyoyi tamkar tatsuniya. Sai dai mambobinsu sun rika aiki dare da rana don karyata zargin da ake musu, suna cewa babu su ko makamantansu. Duk da haka, a 'yan shekarun da suka gabata, wasu daga cikin tsoffin mambobinsu da suka tuba sun fito fili suna tabbatar da cewa kungiyoyin nan na wanzu. Har ma sun fara wallafa littattafai da ke bayyana ayyukan su.

'Yan jarida su ma sun shiga bincike da fallasa wadannan kungiyoyi, suna bankado bayanai masu ban mamaki. Duk da haka, kungiyoyin sirrin sun ci gaba da musanta wanzuwarsu, suna mai da martani da karyatawa. A lokaci guda, an rika samun karin rubuce-rubuce da kira ga jama'a da su nisanci wadannan kungiyoyi, lamarin da ya haddasa tsananin ƙiyayya da zargi ga duk wanda ake tunanin yana da alaka da su.

A ƙoƙarinsu na kare kansu daga wadannan zarge-zarge, kungiyoyin asirin sun fara kamfen don wanke kansu, suna ikirarin cewa ba miyagu ba ne, illa dai suna aiki ne domin kare muradunsu da kuma taimakawa al'umma.

A halin yanzu, wadannan kungiyoyi sun yadu a duniya, wasu suna da rassan kasa da kasa, yayin da wasu ke aiki ne a cikin ƙasashensu kawai. Duk da rufaffen aikinsu, bincike ya nuna cewa suna da babbar tasiri a siyasa, tattalin arziki, da ma rayuwar yau da kullum ta miliyoyin mutane. Zamu ci gaba 

Daga Mujallar Matasa

Follow Us