Katsina Times
Binciken Katsina Times ya tabbatar da cewa har yanzu Sanata Ahmad Babba Kaita na nan a jam’iyyar PDP, domin babu wata sanarwa da ta fito daga gareshi da ke nuna cewa ya fice daga jam’iyyar. Sanata Babba Kaita mutum ne mai ilimi, kuma ya san ka’idojin fita ko shiga kowace jam’iyya. A halin yanzu, babu wata doka ko ka’ida da ya cika da ke tabbatar da cewa ya sauya sheka.
Tun bayan da ya fara siyasa, Babba Kaita yana bin ra’ayin magoya bayansa a duk matakin da yake dauka. Har yanzu ba a ji labarin wani zama da ya yi da mutanensa don tattauna batun barin PDP ko komawa wata jam’iyya ba.
Wata magana da ake dangantawa da jita-jitar sauya shekarsa zuwa SDP ita ce sanya hoton doki a shafinsa na Facebook, tare da rubuta "Da sunan Allah mai jinƙai, mai rahama." Sai dai wannan bai isa a ce ya koma SDP ba.
Binciken Katsina Times ya kuma gano cewa wasu jiga-jigan PDP daga Katsina suna nazarin yiwuwar gyaran jam’iyyar kafin su dauki matakin ficewa daga cikinta.
Sanata Babba Kaita ya wakilci shiyyar Daura a majalisar dattawa na tsawon shekaru shida, kana ya taba zama dan majalisar tarayya na tsawon shekaru takwas. Yana daga cikin sanatocin da jihar Katsina ba za ta taba mantawa da su ba, duba da irin ayyukan ci gaba da samar da guraben ayyuka da ya yi a jihar.
Katsina Times
www.katsinatimes.com