Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Shugaban karamar hukumar Katsina da aka zaba, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya raba tallafin kudi da ya kai Naira miliyan 3.65 ga shugabanni da mambobin jam’iyyar APC a yankin.
An gudanar da rabon tallafin ne a ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, a ofishin jam’iyyar APC na karamar hukumar Katsina. Wadanda suka amfana sun hada da shugabannin jam’iyya, matasa, da sauran al’ummar gari.
A yayin taron, dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba, ya jinjinawa Hon. Miqdad bisa wannan kokari. Ya kuma tuna cewa tun kafin ya zama shugaba, yana bayar da irin wannan tallafi yayin da yake matsayin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai.
Shugaban kwamitin rabon tallafin, Muhammad Sudees, ya bayyana yadda kudaden suka kasu kamar haka:
Shugabannin APC na mazabu 12 – N117,000 kowanne.
Shugaban APC na karamar hukuma – N200,000
Wakilin APC na matakin jiha – N200,000
Kungiyar matasa – N200,000
Kwamandan yakin neman zabe na Kudu II – N150,000
Miqqida Media & Grassroots – N100,000
Kwamitin Ilimi – N150,000
Kungiyar mata ta Kudu II – N50,000
Tallafin Ramadan ga mutum 200 (maza da mata) – N1,350,000
Jimillar adadin kudaden da aka raba: N3,654,000
Da yake jawabi, Hon. Isah Miqdad AD Saude ya bayyana cewa wannan tallafi yana daga cikin kokarin inganta jam’iyyar APC da kuma tallafa wa al’ummar yankin, musamman wadanda suka mara masa baya a lokacin zabe. Ya kuma tabbatar da cewa akwai karin tallafi masu muhimmanci da za a samar nan gaba.
Hakazalika, ya bukaci jama’a su ci gaba da yin addu’a ga Gwamna Malam Dikko Umar, PhD, musamman a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, domin samun nasarar gwamnatinsa.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban APC na karamar hukumar Katsina, Alh. Kabir Usman Amoga, Dr. Kabir Moto, da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Haka kuma, mataimakin shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Usman Yusuf Saulawa, tare da zababbun kansiloli da manyan ‘yan jam’iyyar sun halarci taron.