Katsina Times
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwa kan sacewa da aka yi wa Birgediya Janar Maharazu Ismail Tsiga (ritaya), tare da tabbatarwa iyalansa cewa tana kokari don ganin an kubutar da shi lafiya.
An sace tsohon Darakta Janar na Hukumar NYSC, wanda kuma mamba ne a ACF, yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na ACF, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya fitar, kungiyar ta ce sacewar Janar Tsiga wata alama ce ta yadda matsalar tsaro ke kara tsananta a Najeriya, musamman a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sakkwato da Zamfara.
Duk da cewa ACF ta ki tsoma baki a cikin tattaunawa da iyalan wanda aka sace fili, Muhammad-Baba ya bayyana cewa kungiyar na fahimtar damuwa da bakin cikin da iyalan ke ciki.
"ACF na ci gaba da tuntubar hukumomin jiha da na tarayya, da sauran manyan mutane don ganin an sako Janar Tsiga da sauran mutanen da ‘yan bindiga suka sace ba tare da wani sharadi ba," in ji shi.
Ya kara da cewa kungiyar ta yi Allah wadai da lamarin, yana mai cewa, "wannan abin takaici ne, abin kyama, abin Allah-wadai, kuma abin da ba za a lamunta da shi ba," tare da fatan samun mafita cikin gaggawa.