Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Katsina, Najeriya – 5 Ga Maris, 2025:
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da shirin Rumbun Sauki, wani shiri na gwamnati da ke da nufin rage wahalhalun da ma’aikata, ‘yan fansho da tsofaffi ke fuskanta sakamakon tashin farashin kayayyaki. An gudanar da bikin kaddamarwar a dandalin sayar da kayayyaki da ke gaban Barhim Estate, kusa da Sakateriyar Jihar Katsina. A ranar Laraba 5 ga watan Maris 2025
A jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan shiri yana da matukar muhimmanci ga al’ummar jihar, domin rage matsin lambar da hauhawar farashin kayayyaki ke haifarwa.
"Yau wata rana ce mai matukar muhimmanci a tarihin wannan gwamnati, yayin da muke kaddamar da Rumbun Sauki, wani shiri na musamman da zai rage radadin da ma’aikata da ‘yan fansho ke fuskanta. Dukkanmu mun san irin matsalolin tattalin arzikin da muke ciki, don haka ba za mu tsaya ba muna kallo al’ummarmu na shan wahala," in ji gwamnan.
Shirin Rumbun Sauki zai ba da rangwame na kashi 10% kan manyan kayayyakin abinci kamar shinkafa, fulawa da garin masara domin su zama masu saukin kudi ga jama’a. Gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 4 domin gudanar da shirin, wanda zai fara aiki a cibiyoyi bakwai da ke Katsina, Daura da Funtuwa, kafin daga bisani a fadada shi zuwa dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
A cewar gwamnan, an tanadi tsarin da zai tabbatar da inganci da gaskiya wajen rabon tallafin, inda ma’aikatan gwamnati na jiha da kananan hukumomi, ma’aikatan hukumar ilimi, da ‘yan fansho masu shekaru 60 da sama za su ci gajiyar shirin. Kowane mutum zai iya amfana da kayan tallafin har zuwa kashi daya bisa uku (⅓) na albashinsa ko fanshonsa a wata.
Gwamna Radda ya jinjinawa Injiniya Yakubu Nuhu Danja, Mai Ba da Shawara na Musamman kan Tattalin Arzikin Karkara, tare da dukkan masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen tabbatar da nasarar wannan shiri.
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal Jobe, ya yaba da wannan shiri, yana mai bayyana shi a matsayin babbar nasara ga gwamnatin Radda.
"Wannan shiri na Rumbun Sauki zai ba da tallafi kai tsaye ga ma’aikata da ‘yan fansho, kuma zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci a jihar. Ana sa ran shirin zai haifar da ciniki na kusan Naira biliyan 30 a kowace shekara, wanda hakan zai samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki," in ji Mataimakin Gwamnan.
Ya kara da cewa, shirin zai bai wa ma’aikata damar karbar tallafin kayan abinci ta hanyar rance ba tare da ribar banki ba, inda za a rika cire kudin biyan rancen daga albashinsu a kowane wata.
Shugaban shirin Injiniya Yakubu Nuhu Danja, Mai Ba da Shawara na musamman akan ci-gaban tattalin arziki a karkara, ya jaddada aniyar gwamnati na tabbatar da cewa shirin ya kai ga wadanda suka dace.
"Wannan shiri ne na musamman da Gwamna Radda ya kirkiro domin rage radadin hauhawar farashin abinci. Muna kira ga duk wadanda za su ci gajiyar wannan shiri da su bi dokoki domin ganin an gudanar da shi cikin nasara," in ji shi.
Ya bayyana cewa, a halin yanzu shirin yana kan ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho, amma a nan gaba, gwamnati na shirin fadada shi domin ya shafi sauran al’umma, musamman masu karamin karfi.
Shirin Rumbun Sauki na daga cikin kokarin da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi domin karfafa tsaro na abinci, bunkasa tattalin arziki, da inganta rayuwar al’ummar jihar. Gwamna Radda ya tabbatarwa da al’umma cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsare da manufofi da za su inganta jin dadin jama’a.