Katsina Times
Gwamnatin Jihar Katsina ta karrama fitaccen malamin addini, Shaykh Yakub Yahya Katsina, bisa gudunmuwarsa wajen inganta harkokin lafiya da wayar da kan al'umma kan yaki da cutuka. Bikin karramawar ya gudana a ranar Litinin, 3 ga Ramadan 1446 daidai da 3 ga Maris, 2025, a ofishin Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina, inda aka gayyaci kungiyoyin agaji, malaman addini, shugabannin al’umma da masu rike da sarautun gargajiya.
A yayin taron, gwamnatin jihar ta bayyana rawar da harkar Musulunci ke takawa wajen ci gaban al’umma, musamman ta fuskar bayar da gudunmuwa don yaki da cututtuka masu yaduwa. Bugu da ƙari, an karrama Masarautar Katsina da Shehin Malami, Dr. Isma'il Al-Kashnawy, bisa irin gudunmuwar da suke bayarwa a fannin lafiya.
Taron ya samu halartar manyan kungiyoyin kiwon lafiya da suka hada da WHO, UNICEF, Cigari Foundation, APNET NGO, State Primary Health Care Agency (SPHCA), Emergency Operations Center (EOC), da sauran kungiyoyin agaji na ciki da wajen Najeriya.
Da yake jawabi a madadin Gwamnatin Jihar Katsina, Kwamishinan Lafiya, Alhaji Musa Adamu Funtuwa, ya jinjina wa kungiyoyin da ke tallafawa kokarin yaki da cututtuka, musamman cutar shan-inna (Poliomyelitis). Ya kuma yabawa Shaykh Yakub Yahya kan irin jajircewarsa wajen ci gaban al’umma a fannoni daban-daban.
A madadin malamin, wakilinsa ya karɓi takardar girmamawa daga hannun Kwamishinan Lafiya.
Taron, wanda Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Katsina (SPHCA) ta jagoranta, ya bayyana fatan samun nasarar kawar da cututtuka ta hanyar ingantaccen rigakafi a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.