Sanata Dandutse Ya Bayyana Manyan Ayyuka da Shirye-shiryen Taimakon Al’umma a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02032025_030558_FB_IMG_1740884668480.jpg

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Katsina, Najeriya – 1 ga Maris 2025

Sanata Muntari Muhammad Dandutse, mai wakiltar yankin Funtua a majalisar dattawa, ya bayyana wasu muhimman ayyuka da shirye-shiryen tallafawa al’umma da yake aiwatarwa a yankinsa.

Sanatan ya yi wannan bayani ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Hillside Royal Suites, Katsina, a ranar Juma'a 28 ga watan Febrairu, gabanin rabon kayan abinci da shirin karfafa gwiwar al’umma ta hanyar rabon jari da kayan sana'a da ya aiwatar ranar Asabar da ga watan Ramadan.

Sanata Dandutse ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya fara hidima a matakin gwamnati, ya sha gwagwarmaya don samar da cigaba ga al’ummar yankinsa. Ya ce, “Na fara hidimar jama’a ne tun a matsayin shugaban karamar hukuma, daga nan na zama dan majalisar wakilai na Funtua da Dandume. A yanzu kuma ina wakiltar yankin Funtua mai kananan hukumomi 11a majalisar dattijai.”

Ya bayyana cewa a tsawon shekarun hidimarsa, ya samu nasarori da dama a bangaren gine-gine, ilimi, samar da hanyoyi, gidaje, kasuwanni da kuma bunkasa rayuwar al’umma.

A cewar Sanata Dandutse, a lokacin da yake shugaban karamar hukuma, ya gina shaguna 1,000, gidaje 40, da kuma blok 320 na azuzuwan makarantu a Funtua. Hakazalika, ya gina tituna masu tsawon kilomita 150, kasuwanni da abattoir (wajen yanka dabbobi), da kuma asibitoci don inganta kiwon lafiya a yankin.

A majalisar dattawa, ya bayyana cewa ya samu nasarar kasancewa shugaban kwamitin kula da manyan makarantu na TETFUND, tare da zama mataimakin shugaban Hukumar Raya Arewa maso Yamma (Northwest Development Commission).

Daya daga cikin muhimman nasarorin da Sanatan ya bayyana shi ne kafa sabuwar Jami’ar Kiwon Lafiya da Kimiyyar Likitanci a Funtua. Ya ce:

 “Mun yi kokari tare da Gwamna Dikko Umar Radda, inda aka ware sama da naira biliyan 3 don gina jami’ar. Har ila yau, a kasafin kudin 2025, an ware naira biliyan 5.7 don cigaba da ayyukan gina jami’ar, sannan kuma an ware naira biliyan 5 daga TETFUND.”

Ya ce, wannan jami’a za ta inganta ilimi a Katsina da Arewa maso Yamma, kuma za ta kasance cibiyar da dalibai daga jihohi makwabta za su amfana da ita.

Sanatan ya bayyana cewa ya samar da shirin POS don matasa, inda aka bai wa matasa 400 kayan aiki don su samu abin dogaro da kansu. A cewarsa:

 “Mun hada gwiwa da Taj Bank, kuma cikin watanni hudu kacal, mun samu cigaban kasuwancin da ya kai naira miliyan 450 daga matasan da ke gudanar da ayyukan hada-hadar kudade.”

Haka kuma, ya bayyana cewa matasa 300 sun samu tallafin naira 100,000 kowannensu don sana’ar kiwon kifi, tare da ba da motocin hawa da babura ga shugabannin jam’iyya da jami’an tsaro a yankin.

A kokarinsa na bunkasa harkar noma, Sanata Dandutse ya bayyana cewa ya raba buhunan takin zamani 15,000 ga manoma, malamai, da sauran al’ummar karkara don bunkasa noma a yankinsa. Haka kuma, ya ware naira miliyan 150 domin bai wa mutane 1,000 tallafin naira 10,000 kowannensu don su inganta sana’o’insu.

Yace  “Wani mutum da ke sana’ar zoɓo ya sami tallafin naira 10,000, yanzu kuma ya mallaki gidan kansa. Wannan na nuna cewa idan aka taimaki mutane, za su samu cigaba a rayuwarsu.”

Dangane da matsalolin tsaro, Sanatan ya bayyana cewa ya yi kokari wajen bai wa jami’an tsaro kayan aiki. Ya ce:

 “Mun bayar da sabbin motocin Hilux ga ‘yan banga, mun kuma bai wa kowace karamar hukuma babura biyar don saukaka aikin tsaro a yankunan karkara.”

Ya kuma bayyana cewa ya bai wa rundunar ‘yan sanda da Civil Defence babura domin inganta ayyukansu a yankin.

Sanata Dandutse ya bayyana cewa yana kokarin tabbatar da cewa dukkan kananan hukumomin yankinsa suna da cibiyoyin jarrabawar JAMB domin saukaka wa dalibai samun damar zana jarabawar ba tare da tafiya nesa ba.

Har ila yau, yana kokarin samar da masana’antar sarrafa kayayyakin noma (agro-processing factory) a Funtua, wacce za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.

Sanata Muntari Muhammad Dandutse ya jaddada kudurinsa na ci gaba da aiki tukuru domin bunkasa rayuwar al’ummar yankin Funtua da Katsina gaba daya.

Ya bukaci hadin kai daga shugabanni da al’umma domin ganin an cimma burin da aka sa a gaba na kawo ci gaba mai dorewa.

A ranar Asabar daya ga watan Maris da yayi daidai da daya ga watan Ramadan ne, Sanatan ya raba Shinkafar Azumi, Babura guda dari uku da hamsin da Kekenapep guda dari ga yankunan da yake wakilta.

Follow Us